• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Shugabancin NERC: Barau Yana Kyashin Samar Da Wuta Don Farfado Da Kamfanoni Kano Ne, Sai Munyi Masa Ritaya — Barista S S Umar

BySani Magaji Garko

Nov 11, 2025

Kwararren Lauya kuma Dan Siyasa Barista Salisu Salisu Umar ya ce Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin yana bakin ciki da kyashin ganin an farfado da kamfanonin da suka durkushe a fadin Jihar Kano da samar da cigaban matasa ne ya sa yake kafar ungulu da yin duk mai yuwuwa domin ganin ba’a tantance Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban hukumar kula da harkoki da ka’idojin lantarki ta Kasa NERC.

Salisu Umar ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a Kano, inda yayi Allah wadai da matemakin shugaban majalisar Dattawan saboda rawan da ya taka ganin majalisar bata tantance Ramat domin bashi Shugabancin hukumar ta NERC ba.

“Yanzu Jihar Kano Ina kamfanoni ?, mafi yawa sun durkushe, mafi yawa karancin wutar lantarki ta kashe su, sana’o’i na gida da Mata suke yi sun lalace, wadannan matsalolin kuma sune Barau baya son a farfado da su, kuma muna tabbatar maka wannan makarkashiyar kamar miko mana goron gayyar yaki irin na siyasa ne kuma zamu yake ka har sai mun kaika kasa,” inji Barista Umar.

KU KARANTA: Kwankwaso a 69: Mai Hangen Nesa, Jigo a Siyasar Arewa… Ya Kawo Abba Don Cigaban Kano – Bakwana

“Kujerar Abdullahi Garba Ramat, wata kujera ce da take wakiltar dukkan matasan Nigeria musamman ‘yan asalin Jihar Kano, saboda haka yin adawa da ita kamar yin adawa da cigaban matasan Nigeria ne, kuma sai munyi wa Barau Ritaya a siyasar Nigeria,” inji Umar.

“Kujeru wajen 28 ne za’a bawa ‘yan Kano, kuma mafi yawancinsu duk anga mukami ne kawai na Jeka-nayi-ka shi yasa ba’a damu da su ba, wannan Kujerar da ake son harawa Ramat ita ce kujera babba wacce ake ganin zata amfani mutanen Kano, to ita ma ga su Barau suna neman nesan ta ta da mutanen Kano,” inji shi.

Salisu Umar ya ce matukar aka rasa Kujerar NERC to zasu dauki matakin bibiyar dukkan inda Dan majalisar ya tsaya takara ko Kano da Kudu ko ta Arewa ka takarar Gwamna koma ma takarar shugaban Kasa tare da tabbatarwa baiyi nasa ba, gami da daukar matakan yi masa ritayar Siyasa a Nigeria baki Daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *