Kwamitin masu ruwa na hukumar Hisbah ta Jihar Kano ya ce yunkurin kafa wata kungiya ko hukumar Hisbah Mai zaman kanta wani mataki ne na kafa kungiya da ka iya kawo rarrabuwar kan musulunmi ko sanadiyyar ayyukan ta’addanci a Jihar Kano.
Shugaban kwamitin kuma tsohon shugaban hukumar Hisbah ta Jihar Kano Farfesa Ibrahim Mu’azzam Maibushira ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kano ranar Alhamis.
Maibushira ya ce bayan taron da kwamitin yayi, ya dauki matakin cewa Hisbah Daya ce tak a Kano kuma itace wacce Doka ta amince da ita, idan ya ce an Amince cewa dole ne a dauki matakan da suka da ce kafin korar dukkan wani ma’aikacin Hisbah idan ya aikata wani lefi.
KU KARANTA: Masarautar Kano Ta Nada Abdullahi Bello Gaya Mai-unguwar Hotoro GRA
“An samar da dokar da ta kafa Hukumar Hisbah ta Jihar Kano a shekarar 2003 wacce majalisar dokokin Jihar Kano ta yi, la’akari da damar da sashe 100 na kundin tsarin Mulkin Nigeriya ya bawa majalisar, saboda haka yunkurin wani mutum ko wani kamfanin na kafa Hisbah Mai zaman kanta mu da al’ummar Kano muna ganinsa a matsayin wani yunkuri na siyasa wanda ka iya kawo tashin hankali, rashin zaman lafiya da rasa rayuwan jama’a ko wani abu mai kama da haka,” inji Farfesa Maibushira.
“Muna sanar da al’umma cewa Hisbah bata da alaka da siyasa kuma tana cigaba da ayyukan ta, Amma akwai bukatar gwamnatin Jihar Kano ta kara samar da kayan aiki na zamani da motoci da kuma kula da walwalar ma’aikata don cigaba da HORO DA KYAKYKYAWA DA HANI DA MUMMUNA gami da tsaron rayuwa da dukiyoyin al’umma,” inji shugaban kwamitin.
Ya ce dole ne hukumar ta yi la’akari da Ilimi, sanin yakamata kafin daukar sa a matsayin jami’in hukumar. “Dole ne sauya fasalin yadda ake horar da jami’an Hisbah, dole ne dukkan wani abu da Dan Hisbah yayi hukumar ta dauka a matsayin aikin ta ne saboda haka dole ne kowanne sashi ya bibiyi Yadda wadanda suke a fannin ke gudanar da ayyukan su don gudun aikata barna ko kuma lefi.”
Kwamitin ya kuma shawarci shugabannin hukumar da su tattauna da wadanda ake zargin an kore su ba bisa ka’idaba domin nuna musu illar kafa Hisbah mai zaman kanta da kuma abinda da hakan ka iya haifarwa.