• Wed. Feb 4th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kungiyar Tsofaffun Ma’aikatan Jinya/Ungozoma Ta Tallafawa Gajiyayyu, Masu Tabin-Hankali, Marassa Lafiya 120 a Kano

BySani Magaji Garko

Dec 22, 2025

Kungiyar ma’aikatan Jinya da Ungozoma da suka yi ritaya ta tallafawa Gajiyayyu da masu Larurar Kwakwalwa da marassa lafiya su Kusan 120 a wani yunkuri na ayyukan jin kai da tallafawa mabukata.

Shugaban kungiyar Alhaji Dahiru Ahmed ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci shugabanni kungiyar suka ziyarci gidan Gajiyayyu da masu Larurar kwakwalwa dake unguwar Shahuci da Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad dukka a cikin karamar hukumar Birnin Kano da kewaye.

Shugaban ya ce sun ziyarci gidan gajiyayyun da kuma sashen kula da masu yoyon fitsari na asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ne domin tallafa musu kasancewar ‘ya’yan kungiyar sun kula da irin takura da wahala da masu Larurar ke samun kansu a ciki.

KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa a MAKIA Kano

“Mun tallafawa gajiyayyun su kusan 60 da kayan sawa da sabulai da man shafawa da kuma omo na wanki, sai a nan wajen masu Larurar yoyon fitsari suma wajen 56 mun tallafa musu da dogayen riguna na sawa da sabulai da kayan wanki da man shafawa dukka domin kula da tsaftar jikin su,” inji Ahmed.

Kungiyar ta yabawa gwamnatin Jihar Kano da shugabannin dake kula da gajiyayyu dake gidan na Shahuci da kuma likitoci da jami’an Jinya a sashen kula da masu yoyon fitsari na asibitin Murtala bisa yadda suke kula da tsaftar marassa lafiya a dukkan guraren biyu.

Shugaban ya ce ‘ya’yan kungiyar a shirye suke su bada gudun mowar harar da masu tasowa da bada tallafi musamman idan aka sami ibtila’i ko bukatar temakon gaggawa ta taso.

A jawabinsa, Dakta Amiru Imam Yola na sashin kula da masu yoyon fitsari na asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ya yabawa kungiyar bisa ziyarar da ya ce zata karfafa gwiwar su don cigaba da aikin kula da marassa lafiya.

A cewarsa, a shekarar 2025 kawai, sun yiwa mata aikin yoyon fitsari 450 wanda a dukkan kaso 90 cikin 100 babu wacce ta sake dawowa asibitin don kula da lafiya, yana mai cewa sun yiwa mata 15,000 aiki wanda Kyauta ne kuma mafi yawancinsu an samu Nasara.

Dakta Amiru ya kuma roki shugabanni kungiyar da su rika zuwa lokaci zuwa lokaci don koyawa ‘yan baya dabarun aiki la’akari da irin kwarewar da suke da ita.

Likitan ya ja kunnen al’umma da su guji barin mata suna yin doguwar Jinya wanda a cewarsa ita babbar matsalar da take kawo Larurar yoyon fitsari, yayin da ya roki mahukunta da su rika samar da isassun kayan kula da mata masu juna da haihuwa.

Shima, shugaban gidan gajiyayyu da masu Larurar kwakwalwa dake Shahuci Malam Yusuf Sani godewa kungiyar yayi bisa ziyarar inda ya ce zata karfafa gwiwar ma’aikata da mazauna gidan baki daya.

Ya ce wasu daga cikin matsalolin da suke fuskanta shine yadda al’umma ba sa son ziyartar gidan duk da mazauna gidan na bukatar ziyarar domin tattaunawa da gami da tallafa musu.

Ya roki al’umma da su rika tallafawa masu bukata ta musamman da masu karamin karfi don samun lada a gurin Allah da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *