• Wed. Feb 4th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Dan Majalisar Dokokin Kano Sarki Aliyu Daneji Ya Rasu

BySani Magaji Garko

Dec 24, 2025

Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano Alhaji Sarki Aliyu Daneji ya rasu sakamakon rashin lafiya.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafukansa na sada zumunta.

KU KARANTA: Kungiyar Tsofaffun Ma’aikatan Jinya/Ungozoma Ta Tallafawa Gajiyayyu, Masu Tabin-Hankali, Marassa Lafiya 120 a Kano

Daneji ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a Kano.

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce rasuwar Daneji ta zo ne ‘yan awanni bayan rasuwar takwaransa mai wakiltar karamar hukumar Ungogo Alhaji Aminu Sa’adu Ungogo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *