• Wed. Feb 4th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

2025: Hisbah Ta Karbi Korafi 12,446, Ta Yi Sulhu 1,908, Ta Karbo Hakkin Mutane Sama Da Miliyan 145 a Kano

BySani Magaji Garko

Jan 2, 2026

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta Karbi Korafe-Korafe da adadinsu ya kai guda 12,446 tare da yin Sulhu a Korafe-Korafe 1,908 a shalkwatar hukumar da kuma Ofisoshinta na kananan hukumomin Jihar Kano 44 dukka a shekarar 2025 da ta gabata.

Haka kuma, hukumar ta kai Manya-manyan sumame sau 9 inda ta kama mutane 132 a gurare daban-daban a ciki da wajen kwaryar Birnin Kano.

Dakta Mujahideen Amenuddeen, Mukaddashin kwamandan hukumar ne ya bayyana hakan cikin wata kididdigar bayanai da ya aikowa da jaridar GLOBAL TRACKER ranar Juma’a da safe.

KU KARANTA: Kotu Ta Umarci Bankin UBA Ya Kwace Kudin Kano Da Ake Zargin An Karkatar Da Su

A cikin kididdigar, hukumar ta ce mutane 93,231 ne suka kai ziyara ko dai ta aiki ko bada bayanai ko kuma wasu dalilai daban-daban da suka shafi ayyukan ta.

Haka kuma hukumar ta sami manyan lefuka 4,246 a shalkwatar hukumar da Ofisoshinta na kananan hukumomi wanda kusan dukkaninsu ta mikawa rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ko hukumar da abin ya shafa domin cigaba da gudanar da bincike gami da daukar matakan da suka dace.

Hakazalika, hukumar ta Karbi kudade da adadinsu ya kai naira miliyan 145,406,409 wanda kusan dukkaninsu hakkin mutane ne ko dai na shayarwa ko kuma na Bashi lamarin da ya sa tuni aka mikasu ga masu hakkin don aiwatar da umarnin Allah madaukakin Sarki.

Dakta Mujahideen ya bukaci kungiyoyi da hukumomi da al’umma da daidaikun mutane da su cigaba da yin aiki kafada-da-kafada da hukumar Hisbah ta Jihar Kano don yin hani wajen aikata munanan ayyuka da horo da kyakykyawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *