• Wed. Feb 4th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Yarjejeniyar Tinubu Da Isra’ila Cin Amana Ce Ga Tsayayyar Manufar Nigeria Ta Yaki Da Zalunci Da Ta’addanci  Da Danniya

BySani Magaji Garko

Jan 5, 2026

FASSARA: NASIRU MOHAMMED WAZIRI, KANO

nasirumuhammedwaziri@gmail.com

A jajiberin rahoton da ke nuna yiwuwar harin sojin Amurka a kan Nijeriya a ranar Kirsimeti, ‘yan Nijeriya sun wayi gari da wani lamari mai tayar da hankali ƙwarai, wannan karon daga Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.

A wata sanarwa da ta haifar da fargaba a faɗin duniya, Netanyahu ya bayyana aniyar Isra’ila ta “kare Kiristoci a Nijeriya,” wata magana da ke raunana tsarin mulkin Nijeriya na rashin fifita wani addini, tare da wargaza dogon tarihin ƙasar na zaman tare tsakanin addinai daban-daban.

Wannan furuci bai zo shi kaɗai ba. Ya biyo bayan tarurruka masu girma sama da guda shida tsakanin jami’an Isra’ila da gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga Mayu 2023 zuwa Disamba 2025.

Rahotanni sun nuna cewa waɗannan tattaunawa sun fi mayar da hankali kan haɗin gwiwar tsaro, fasahohin sa ido, musayar bayanan sirri, da yaƙi da ta’addanci.

A ranar 22 ga Agusta, 2025, Ƙaramar Ministan Harkokin Waje ta Nijeriya, Ambasada Bianca Ojukwu, ta rattaba hannu kan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tsaro da Mataimakiyar Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz.

Yarjejeniyar ta ƙunshi musayar bayanan sirri, horo kan yaƙi da ta’addanci, da faɗaɗa haɗin gwiwar soja.

Shekara guda kafin haka, Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta karɓi Ambasadan Isra’ila a Nijeriya, Michael Freeman, wanda ya sanar da shirin kafa cibiyoyin “ƙirƙira” guda talatin domin mata ‘yan Nijeriya.

Duk da cewa an lullube waɗannan shirye-shiryen da harshen haɗin kai da kyakkyawar niyya, a zahiri suna zama dabarun tasiri na siyasa (soft power) da nufin gyara mummunan sunan Isra’ila a idon duniya.

Wadannan al’amura suna haifar da muhimmiyar tambaya: wace irin daidaituwar ɗabi’a ko dabarun siyasa ce yanzu ke haɗa Nijeriya da Ƙasar Isra’ila, ƙasashe biyu da a tarihi suka bambanta ƙwarai a manyan batutuwan duniya, na ɗabi’a da na diflomasiyya?

Ƙarfafa alaƙa da Isra’ila a wannan lokaci ba kuskuren dabara kaɗai ba ne, illa ma babban gazawar ɗabi’a.

A tarihi, Nijeriya ta kasance ƙasar da ke kare ‘yancin addini, zaman tare tsakanin al’umma, da adawa da mulkin mallaka. Isra’ila kuwa, ta fuskanci suka masu tsanani daga ƙasashen duniya kan ayyukan wariya, ciki har da takaita bautar Kiristoci, kai hare-hare kan limamai, da rusa wuraren tarihi na Kiristanci a Urushalima da Gaza.

Saboda haka, kusantar da ke ƙaruwa tsakanin Abuja da Tel Aviv ba abin mamaki kaɗai ba ne, abin tayar da hankali ne matuƙa.
Tun daga Oktoba 2023, hare-haren sojin Isra’ila a Gaza sun haifar da mummunar bala’in jin ƙai da ba a taɓa ganin irinsa ba tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.

An lalata unguwanni gaba ɗaya; an rushe asibitoci, makarantu, masallatai da coci-coci; kuma kusan kashi casa’in cikin ɗari na al’ummar Gaza sun rasa matsugunansu. Aƙalla Falasɗinawa 71,266 aka kashe, sama da 171,000 suka jikkata, mafi yawansu mata da yara. Abin da ke faruwa hukunci ne na gama-gari a mataki mai girma.

Kalaman manyan jami’an Isra’ila sun ƙara tabbatar da wannan manufar ciki har da amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi.

Tsohon Ministan Tsaro Isra’ila Yoav Gallant, ya kira Falasɗinawa “dabbobin mutane” yayin da ya sanar da cikakken killacewa ba abinci, ba ruwa, ba mai.

Ministan Harkokin Waje, Israel Katz, ya yi barazanar hana Falasɗinawa ko “ɗigon ruwa” guda ɗaya. Waɗannan kalamai, tare da ta’asar da sojojin Isra’ila suka aikata a Gaza, sun sa fitattun masana nazarin kisan kare dangi har da masana ‘yan Isra’ila suka bayyana cewa kisan da ake yanzu haka a Gaza misali ne karara na kisan kare dangi.

Fitaccen masani, Omer Bartov, ɗan Isra’ila, ya ce: “Na san kisan kare dangi idan na gan shi. Abin da na kammala babu shakka shi ne Isra’ila na aikata kisan kare dangi a kan al’ummar Falasɗinu.” Duk da ikirarin tsagaita wuta, Isra’ila ta ci gaba da hare-haren kisa tare da hana ayyukan kungiyoyin jin ƙai sama da talatin, ciki har da Médecins Sans Frontières (MSF), lamarin da ya ƙara tsananta abin da hukumomin agaji ke kira “bala’in jin ƙai da ba za a iya misaltawa ba.”

Manufar harkokin wajen Nijeriya a da ta ginu ne a kan jagorancin ɗabi’a. Ƙasar ta tsaya tsayin daka wajen yaƙi da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, ta tallafa wa gwagwarmayar ‘yanci a Afirka, kuma ta samu girmamawa a duniya ta hanyar tsayawa tare da waɗanda ake zalunta, ba masu zalunci ba.

Yanzu dai wannan tarihi kamar ya zama labarin da ya shuɗe. Tun bayan hawar Shugaba Tinubu mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, hulɗar Isra’ila da Nijeriya ta ƙaru ƙwarai. Ziyartar diflomasiyya na zuwa tare da alkawuran musayar bayanan sirri, horo kan yaƙi da ta’addanci, da haɗin gwiwar soja.

Wannan yana haifar da tambaya mai razana:

Wacce irin akidar tsaro ce Isra’ila ke fitarwa zuwa Nijeriya?

Harin bama-bamai ba tare da bambanci ba?

Killacewar yankuna?

Kai hari kan ‘yan jarida?

Rushe gadon al’adu da tarihi?

A daidai lokacin da Afirka ta Kudu ke jagorantar shari’a a Kotun Duniya ta ICCJ kan Isra’ila saboda zargin kisan kare dangi, kuma yayin da yawancin ƙasashen Afirka, Asiya da Latin Amurka ke Allah-wadai da ayyukan Isra’ila, Nijeriya ta zaɓi ƙara kusanci da Tel Aviv.

Wannan sauyi ya zo daidai da sabuwar magana daga Shugaban Amurka, Donald Trump, wadda ke bayyana rikicin tsaron cikin gida na Nijeriya a matsayin “kisan Kiristoci” wani sauƙaƙa al’amari mai haɗari da ke karkatar da gaskiyar matsalolin Nijeriya. Rage matsalolin tsaron Nijeriya zuwa labarin tsangwamar addini, kamar yadda Trump da Netanyahu suka yi, rashin gaskiya ne babba.

Dabara ce ta siyasar duniya da ke barazanar hura wutar rikicin addini domin cimma muradun waje.

Harba bama-bamai a wurare a Sokoto mazaunin Halifanci kuma jiha mai rinjayen Musulmi na nuna hatsarin irin wannan fahimta.

Yiwuwa Shugaba Trump, wanda ke ikirarin kare “Kiristocin da ake tsanantawa,” tare da haɗin gwiwar Isra’ila da wasu ƙasashen yamma, ya halasta tsoma bakin soja a Nijeriya a ranar Kirsimeti, na ɗauke da sakamako mai girman gaske da zai iya girgiza ƙasar.

Irin wannan mataki na iya zurfafa rarrabuwar kabilanci da addini tare da shigo da rikice-rikicen waje cikin yanayin cikin gida mai rauni.
Ba abin mamaki ba ne, waɗannan al’amura sun ƙara tsananta shakku a tsakanin jama’a game da alaƙar kusurwoyi uku da ke tasowa tsakanin gwamnatin Tinubu, Amurka, da Isra’ila, duk da musanta hakan a hukumance.

Nazari mai zurfi kan jerin abubuwan da suka faru na nuna wata hanya mai tayar da hankali wadda ke nuna yadda ƙasashen waje ke samun rinjaye fiye da kima a kan manufofin tsaro da harkokin wajen Nijeriya.

A yau, Nijeriya tuni na fama da rarrabuwar addini da rikice-rikicen kabilanci da yankuna, matukar wanna alaka ta cigaba to akwai fargabar Nigeriya na iya shiga halin ha’ula’i.

Original Copy by Professor Siddiq Abubakar Mohammed.

Daga: Cibiyar Cigaban Dimokuradiyya, Bincike Da Horo.

Zaria, Kaduna State, Nigeria.
Imel: info@ceddert.org

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *