• Wed. Feb 4th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Shugaban Zakka Da Hubusi Ya Taya Gwamnan Kano Murnar Cika Shekaru 63 Da Haihuwa

BySani Magaji Garko

Jan 6, 2026

DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

Shugaban Hukumar Zakka da Hubsi ta Jihar Kano Sheikh Barista Habibu Muhammad Dan-almajir Fagge ya taya gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf murna cika shekaru 63 da haihuwa.

A cikin sakon taya murnar, shugaban Hukumar Dan-àlmajiri ya bayyana cewa gwamnan ya kasance shugaba mai tausayi da Hangen nesa da Adalci da kuma kishin alummarsa, wanda manufofinsa ke ci gaba da kawo sauyi a fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar jihar Kano.

KU KARANTA: 2025: Hisbah Ta Karbi Korafi 12,446, Ta Yi Sulhu 1,908, Ta Karbo Hakkin Mutane Sama Da Miliyan 145 a Kano

Barista ya ce jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen aiwatar da ayyuka daban-daban don samar da ci gaba da kuma shugabanci wanda ya maida hankali kan rayuwar alumma, na daga cikin abubuwan da ke karfafa gwiwar ma’aikatan gwamnati wajen yin aiki tukuru domin ciyar da jihar gaba.

Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya kara wa gwamnan lafiya, ya kuma yi masa jagora tsawon rai, da kuma hikima domin samun damar sauke nauyin da Allah dora masa da kuma jagorantar Jihar Kano zuwa matakin cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *