• Wed. Feb 4th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

KNCDC Ta Gudanar da Bincike, Wayar da Kan Jama’a Bisa Barkewar Wata Cuta a Kano.

BySani Magaji Garko

Feb 1, 2026

Hukumar dakile Yaduwar Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) ta gudanar da ayyukan tantance marasa lafiya, kula da lamurra, wayar da kan al’umma, da kuma tattara samfuran gwaje-gwaje a kauyen Gamji da ke gundumar Zakarawa a karamar hukumar Garko, biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu mazauna yankin sun rasu sakamakon zargin kamuwa da cutar Diphtheria da Cutar Sankarau.

An gudanar da wannan aikin ne domin tantance sahihancin rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka yada da kuma duba halin lafiyar al’ummar yankin.

A cikin wata sanarwa da Aminu Ibrahim Abdullahi, mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na KNCDC, ya fitar a madadin shugaban hukumar Farfesa Muhammad Adamu Abbas, wadda aka aikawa da GLOBAL TRACKER a Kano ranar Lahadi, ya bayyana cewa hukumar ta tura tawagar kwararrun likitoci da masana harkokin lafiya zuwa kauyen Gamji domin gudanar da bincike kai tsaye da daukar matakan gaggawa.

KU KARANTA: Ana Shirin Zanga-zangar Neman Hakkin Iyalan Mafarautan Kano Da Aka Yiwa Kisan Gilla A Edo

Sanarwar ta ce, a yayin aikin da aka gudanar ranar Asabar, tawagar KNCDC ta gudanar da cikakken binciken ilimin yaduwar cututtuka (epidemiological assessment) a cikin al’ummar yankin.

An raba tawagar zuwa rukuni guda hudu, inda kowanne rukuni ya zagaya gidaje-gidaje domin gano masu fama da rashin lafiya, tantance su, da kuma kula da su, ta yadda babu wani gida da za a bari a baya.

An gano mutanen da ke nuna alamun rashin lafiya, an duba lafiyarsu sannan aka dauki samfuran gwaje-gwaje daga gare su domin tabbatar da musabbabin cututtukan.

Baya ga tattara samfuran, tawagar ta raba magunguna kyauta ga wadanda abin ya shafa a matsayin matakin gaggawa, tare da ba wa iyalai shawarwarin kiwon lafiya kan yadda za su kula da marasa lafiya da kuma yadda za su kare kansu.

Hukumar ta ce ziyarar na da nufin rage barazanar lafiyar jama’a, inganta lafiyar marasa lafiya, da kuma hana yaduwar cututtuka masu saurin kamuwa a cikin al’umma.

Haka kuma, tawagar ta tara mazauna kauyen domin wayar da kan su muhimmancin zuwa asibitoci da wuraren kiwon lafiya da zarar sun lura da alamun rashin lafiya.

An shawarci al’umma da su rika kai rahoto ga asibitoci ko jami’an lafiya na yankinsu idan sun yi zargin barkewar wata cuta, domin a dauki matakan gaggawa.

Bugu da kari, jami’an KNCDC sun kai sakon wayar da kai zuwa masallatai a yankin, inda suka ilmantar da jama’a kan hanyoyin kare kai daga cututtuka, muhimmancin kai rahoto da wuri, da kuma hadin kai da hukumomin lafiya a lokacin da ake fuskantar barazanar lafiyar jama’a.

A karshe, Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudurinta na kare lafiyar al’ummar jihar baki daya, tare da tabbatar da cewa KNCDC za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin har sai sakamakon gwaje-gwajen dakin bincike ya fito, wanda zai jagoranci daukar karin matakai idan bukatar hakan ta taso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *