Bayan yunkurin kama shi banyi Nasara ba, tsohon jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai zai bayyana a gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa EFCC a ranar Litinin.
Lauyan El-Rufai Ubong Esop Akpan ne ya bayyana hakan, yayin da yake mayar da martani kan yunkurin jami’an tsaro na kama El-Rufai a filin jirgin saman Abuja.
KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: Hukumar EFCC Ta Tsare Gudaji Kazaure
Ubong Esop Akpan ya ce EFCC ta kai takardar sammaci gidan El-Rufai lokacin da yake kasar waje, amma sun sanar da EFCC cewa da zarar ya dawo Najeriya zai amsa gayyatar.
Ubong Esop Akpan ya kara da cewa abun takaici ne yadda jami’an tsaro suka yi yunkurin kama El-Rufai a filin jirgin sama, yana mai cewa ba zasu lamunci hakan ba.
DAILY NIGERIAN