• Thu. Apr 9th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

An Ga Watan Ramadan a Saudiyya

BySani Magaji Garko

Feb 17, 2026

Kasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan azumin watan Ramadan na bana, wanda hakan ke nufin za a fara azumin daga gobe Laraba 17 ga watan Fabrairu a ƙasar ta Saudiyya.

Shafin sada zumunta na manyan masallatan kasar wato Haramain ne ya sanar da haka a kafar X, inda shafin ya ruwaito cewa, “an ga jinjirin wata a ƙasar Saudiyya. Don haka za a fara azumin wata Ramadan na shekarar 1447 daga gobe,” kamar yadda sanarwar ta nuna.

Tuni dai hukumomi a Najeriya suka buƙaci musulman ƙasar su nemi jinjirin watan a yau Talata 17 ga Fabrairu 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Sha’aban 1447AH.

KU KARANTA; Ƙasashen Musulmi na taron Gaggawa a Saudiyya Don Daukar mataki kan Kona Al’qur’ani a Sweden

Buƙatar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar.

Sanarwar ta buƙaci Musulmi su fara neman jinjirin watan azumi a wannan rana, tare da umartar duk wanda ya ga watan da ya kai rahoto ga shugaban ƙaramar hukuma ko Dagaci mafi kusa domin a isar da saƙon ga fadar Sarkin Musulmi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *