Ni a waje na tsarin dimukuradiyya ba wai kawai ya na nufin abinda ya shafi yawan lambobin mabiya ba kawai. Za a iya cewa shi tsari ne da kuma ya shafi daidaituwar al’amurra, yin tsinkaye da hakurin zama da juna, duk a wani yanayi mikakke kuma lafiyayye.
Bari in tafi kai tsaye ga makasudin wannan rubutun. Wato abubuwan yabawa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, ke yi, bayan shigowar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC.
Da ganin yadda Sanata Barau ke ta kai-wa-da-komowa kan al’amuran jam’iyyar ka san lallai babban burinsa shine kara karfafa jam’iyyar, samun nasarar ta a zabukan 2027 da kuma mayar da APC din abar kauna ga kowa. Saboda nasarar samar da tsayayyun manufofi.
Ai wato jama’a ba su ma gama tsinkewa da lamarin Sanata ba sai lokacin da ya fada a gaban kowa cewar, shi fa ya sarayar da tasa takarar ta neman gwamna. Ya fadi hakan ne kwanan baya kadan lokacin karbar gwamnan zuwa ga jam’iyyar APC. Kuma fa ya yi hakan ne bisa radin kansa.
Bai tsaya a nan ba sai da ya bayyana cewar, yanzu duk karfinsa ya na bayan gwamna mai ci Abba Kabir Yusuf. Kan ya samu ya maimaita. Ya kuma umarci dukkan magoya bayansa da su yi haka su ma. Yin hakan kuwa na daga cikin samun tushen hadin kai a cikin jam’iyyar.
Idan jama’a ba su manta ba, bayan Sanatan ya fadi matsayin sa ne kan goyon bayan gwamna Abba, a dai lokacin wancan biki, sai tsohon gwamnan na Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, CON, a cikin nasa jawabin ya ce, ya gama magana da dukkanin wadanda ke son tsayawa takarar na gwamna, dukkansu sun janye aniyar takarar ta su sun bar wa shi gwamnan mai ci, Abba.
A nan ina ga ba wai Ganduje ne kadai ya kamata a jinjinawa ba, ya na da kyau a ce su ma ‘yan takarar an jinjina musu. Dan kuwa wannan ma wani hobbasa ne na nuna son hadin kan jam’iyya da neman kara karfafa ta da kuma nuni wajen yin biyayya ga tsarin shugabanci.
Wadanda kowa ke kawowa a kansa da Ganduje ya fadi waccan magana sune, Maigirma Nasiru Yusuf Gawuna da kuma Maigirma Murtala Sule Garo. Gaskiyar zance dole su ma a jinjina musu. Gaba dayansu su na nuni da cewa, ita fa harkar, ba fa ta ko-a-mutu-ko-rai ba ce. Idan ma akwai wasu masu son tsayawa takarar, bayan wadannan, to ba za a iya fadar su kai tsaye a ce da wane da wane ba. Wannan shine gaskiyar zance.
Ni a gani na, jam’iyyar APC da jagororin ta sun yi wa gwamna hakan ne dan ya kara samun nutsuwa a harkar. Sannan kuma su kara nuna masa cewar, yanzu fa an zama daya, ba tare da wata fargaba ba.
Ina ga watakila dalilin ma da ya sa a ka fito da wani sabon take kenan, na “Kano First.” Dan nuni da cewar Kano kadai a ka sa a gaba. Ba maganar wata adawa ko hamayya ko rashin amincewa juna ba. Kano kawai.
Wani abinda na fara lura da shi kuma shine, shi da kansa Maigirma gwamna ya fara sakankancewa da tsarin tare da yin abinda ya dace daga bangaren sa. A nawa nazarin fa nake magana.
Mun ga yadda ya rungumi tare da kara kyautata tsarin kaso na shugabancin jam’iyya a matakin mazabu da kananan hukumomi. Ni dai har zuwa yanzu ban ji wajen da gwamna ya yi katsalandan ba. Idan na yi kuskure a gyara min.
A nawa nazarin, gwamna na yin abubuwan sa ne yadda ya dabi’antu da yin su. Na san dai kowane mutum, ya na da irin nasa yanayi da tsarin yadda yake tafiyar da al’amurransa. Babban abin bukata kawai shine taya juna da addu’a.
Ta fuskar Sanata kuma da ragowar jagorori, dole ne ka yaba musu ganin yadda suke kai gwauro su kai mari wajen kara karfafa jam’iyyar tare da kyautata harkokin mulki. A dalilin haka, ina ga ba zan yi kaffara ba idan na ce Sanata Barau, a yadda a ke ciki yanzu, na daya daga cikin kwakwalen dake yin hobbasar ganin an samu kyakkyawan yanayi da hadin kai cikin APC a jihar Kano. Wannan ba-wai-ba-inke.
In an kula da kyau za a iya tuna cewar, daga lokacin da ya fadi janyewa daga takarar gwamna, sai a ka ga ya kara daura damara sosai wajen bayar da amintaccen goyon baya na bukatar samun nasarar APC da gwamna a wannan kakar zabe da take daf da shigowa.
Yanzu misali mu kalli yadda ya yi rabon ababan hawa ga shugabancin APC daf da amsar gwamna Abba cikin jam’iyyar. Ya rarraba ga shugabannin APC na yankin da yake wakilta, wato Kano ta Arewa. Bai tsaya a nan ba kawai, sai da ya je ya tattaba shugabancin na ragowar shiyyoyin.
Wannan fa ba ma a maganar ababan hawa da ya ba wa shugabannin mulki na kananan hukumomi 13 na yankin sa na Kano ta Arewa. Daf da zan yi wannan fassarar rubutu na daga Turanci zuwa Hausa, na ga an ce ya kara yin ruwan saman ababan hawa ga shugabannin kananan hukumomin shiyyarsa. Wato wasu kayan sai amale!
Duk kuma fa abubuwan alheri din nan da yake yi, ya na yi ne ga kowa. Ba ruwan sa da wai cewar wadannan tsofaffin ‘yan APC ne, ko kuma wadannan sune sabbin ‘yan APC da su ka shigo kwanan nan da gwamna. Shi a wajen Barau dukkansu daya suke. Tun da dai dukkansu yan jam’iyyar APC ne.
Kuma fa wani abin ban sha’awa ga wannan Sanatan shine, balagarsa a siyasa ta kai ya fahimci cewar, goyon bayan wani tsari ko tafiya ko yanayi, bisa doron doka, a dimukuradiyya halas ne. Haka ma kuma ya fahimci cewar yin adawa da kalubale da kushen yanayi ko tsari ko wata tafiya, shi ma bisa doron doka da oda, halas ne.
Wani babban abin ban sha’awa kuma da na ci karo da shi shine, da yawa daga cikin mutanen bangaren gwamna Abba da su ka shigo da shi daga NNPP zuwa APC, sun yarda kuma sun sakankance cewar Sanata Barau da gaske har cikin zuciyarsa ya na son ganin samun nasarar gwamnan da gwamnatinsa a wannan tafiyar da a ke ciki.
Sannan wani babban abin lura kuma shine, Sanata Barau ya yarda cewar samun nasarar gwamna, samun nasarar APC ce.
Anwar ya rubuto wannan daga Kano
Alhamis, 26 ga watan Fabrairu, 2026