Ana zargin cewa Harin da Kasashen Amurka da Isra’ila suka kai ya yi sanadin Mutuwar jagoran Addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei.
Khamenei dai shine babban kwamandan Askarawan dukkan rudunonin sojan kasar ta Iran.
Firi Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ne dai ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
KU KARANTA: Yakin Isra’ila da Iran: Trump Na Kokarin Yin Kuskuren Da Tsohon Shugaban Amurka Bushi Ya Yi’
Sai dai Babu wata majiya da zata tabbatar da lamarin ko akasin hakan.
Shima shugaban Amurka Donald Trump ya ki yadda da majiyoyin da suka tabbatar da rasuwar Khamenei.
A wani hoto da jaridar GLOBAL TRACKER ta gani da ya fito daga ofishin tattara bayanai na shugaban Amurka (Situation Room) ya ce mista Trump bai gamsu da majiyoyin da suka tabbatar da Mutuwar Ayatollah Khamenei ba.
“Ni ban gamsu da Mutuwar Khamenei ba, kai ko da ya mutu, ya kashe kansa ne domin ya janyo dukkan mabiya shi’a na Duniya su dauki yaki da Amurka da Isra’ila,” inji Trump.
To Amma majiyoyi da kafofin yada labarai na Iran sun musanta Mutuwar Khamenei.