Hare-haren kasashen Amurka da Isra’ila ya yi sanadin mutuwar tsohon shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad.
Majiyoyi da kafofin yada labaran Iran sun tabbatar da mutuwar Ahmadinejad da sauran wasu masu temaka masa.
Hakazalika, kwararren Dan Jarida kuma masanin tsaro a yankin gabas ta tsakiya “Megatron” ya tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar.
KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: Ana Zargin Harin Amurka Da Isra’ila Ya Yi Sanadin Mutuwar Ayatollah Khamenei
Ahmadinejad dai ya Mulki Iran daga shekarar 2005 zuwa 2013.
A bara yayi takarar shugabancin kasar Amma majalisar koli ta harkokin Addinin Iran wacce Ayatollah Ali Khamenei ya ke jagoranta da ki tantance shi.