Kasar jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ce zata bawa kowanne jirgin kowacce kasa a duniya damar wucewa ta mashigar ruwan “Hormuz” matukar kasar ta Kori Jakadan kasashen Amurka da Isra’ila daga kasarta.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Aragchi ne ya bayyana cikin wata sanarwa da ta ambato rundunar juyin juya Hali ta Iran IRGC na bayyana hakan a matsayin wata yarjejeniya da kasashen dake yankin ka iya cimma koda ba’a tsagaita Wuta ba.
Daukar matsayin dai na nufin Iran tana son larabawa su sake katse huldar jakadanci da kasashen Amurka da Isra’ila, wanda wasu kewa kallon shirin mayar da Isra’ila saniyar ware a yankin gabas ta tsakiya.
KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: Isra’ila Da Amurka Sun Kashe Tsohon Shugaban Kasar Iran Ahmadinejad
A wani cigaban labarin kuma, wani mai magana da yawun Khatam al-Anbiya, babban kwamiti na hadin gwiwar sojin Iran, ya yi barazanar cewa Iran za ta kai hari kan bankunan Isra’ila da na Amurka a yankin a matsayin ramuwar gayya bayan Isra’ila da Amurkan sun kaiwa wani bankin Iran hari.
Ebrahim Zolfaghari ya gargaɗi cewa “mutane a yankin kada su kusanci bankuna daga nisan kilomita ɗaya,” kamar yadda gidan talabijin na gwamnatin Iran, IRNA, ya ruwaito.
“Abokan gaba sun ba mu ‘yancin kai hari kan cibiyoyin tattalin arziki da bankuna” mallakar Amurka da Isra’ila, in ji Zolfaghari.
Haka kuma, IRNA ya ruwaito cewa an kai hari kan wani gini na Bankin Sepah, bankin gwamnati dake Tehran.
Kafafen yada labaran Iran sun ruwaito cewa an samu wasu matsaloli a ayyukan Bankin Sepah da wani bankin gwamnati me suna Melli.