Al’ummar garuruwa kusan 20 a karamar hukumar Dawakin kudu a Jihar Kano sunyi Zanga-zanga gami da yin Allah-wadai da yadda wani kamfanin hakar dutse ke yin amfani da nakiya mai karfin da ya wuce Kima don fasa dutse lamarin da ya ke janyo rushewar gidajen al’ummar yankin.
A zanga-zangar da suka yi a garin Gano, al’ummar garuruwan sun bukaci mahukunta a yankin da su saka baki domin kawo ƙarshen lamarin yana mai cewa gaza samar da masalaha a Al’amarin ka iya janyo tashin hankali gami da aikata lefuka a yankin.
Wani jigo daga cikin masu zanga-zangar Malam Rabiu Auwalu Tukur a wani bidiyo da GLOBAL TRACKER ta gani ya bayyana cewa a mafi yawan lokuta suna kokarin Jan hankalin jama’a karsu dauki doka a hanunsu, yana mai cewa matukar mahukunta basu dauki matakin da ya kamata ba, al’ummar yankin za su yi gaban kansu.
KU KARANTA: Sanata Barau Da Hadin Kan APC a Kano — Abba Anwar
Ya ce gururuwan da abin ya shafa sun hada da Gano da Fallau da Basarma da Bena da Asiyaya da Basarma da Dinya da Dashira da Nera da Bakarawa da Dumar Rafi da Gogar da Dashira da sauransu.
“Matukar mahukunta suka Gaza daukar mataki, zamu dukufa da yin addu’o’i Allah ya durkusar da kamfanonin su kasa Jindadin kamfanonin, duk wanda yake da hanu Allah ya rusa shi,” inji Tukur.
“Gaba Daya al’ummar yankin an hanamu zaman lafiya, duk lokacin da aka buga nakiya sai gidaje sun tsage wasu lokutan ma su rushe, fulanin da suke kusa da yankin idan an buga nakiya wasu lokutan firgicewa suke su kama guje-guje lamarin da yake saka wasu dabbobin su bata,” inji Rabi’u.
“Muna kira ga Dagatai da Hakimai da masu unguwa, da shugaban karamar hukuma da ‘yan majalisar tarayya da Jiha da sanatoci da gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da su kawo mana dauki domin al’ummar wannan yanki muna cikin wahala, kuma matukar mahukunta basu dauki mataki ba to dole za’a samu karya doka a wannan yankin,” inji Tukur Rabi’u.
Masu zanga-zangar sun bukaci mahukunta a yankin da su dauki mataki, yana mai cewa matukar aka gaza samun matsaya al’ummar yankin zasu daki mataki da kansu.