• Thu. Apr 9th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kwankwaso Da Magoya Bayansa Sun Koma Jam’iyar ADC

BySani Magaji Garko

Mar 30, 2026

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano ya koma jam’iyyar haɗaka ta ADC tare da magoya bayansa bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.

An gudanar da bikin komawarsa ne a gidansa da ke Kano, inda shuwagabannin jam’iyyar da dimbin magoya bayansa suka hallara domin tarbar sa.

Tsohon gwamnan ya kuma buƙaci magoya bayansa su yi rajistar jamʼiyyar, tare da samun katin zaɓe na ƙasa.

KU KARANTA: Kwankwaso Na Tattaunawa Da Jam’iyar ADC Kafin a Shirye-shiryen Zaben 2027

A jiya ne Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga NNPP, yana mai cewa matakin na daga cikin kokarin haɗa kai da wasu jam’iyyu domin kawo sauyi a ƙasar.

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a samar da hadin gwiwa tsakanin manyan ‘yan adawa, domin tinkarar kalubalen da Ƙasar ke fuskanta da kuma inganta shugabanci.

Sai dai har yanzu ɓangaren NNPP ba su fitar da wata sanarwa mai karfi kan ficewar tasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *