• Wed. Jul 16th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mutane 7 Sun Mutu a Zanga-zangar Bayan Zaɓe a Mozambique

BySani Magaji Garko

Nov 14, 2024

Mutane 7 ne rahotanni suka ce sun mutu yayin da wasu da ba’a san adadinsu ba suka jikkata sakamakon zanga-zangar da ta balle a lardin Nampula dake arewacin kasar bayan zaben shugaban kasa a Muzambique.

An gudanar da zaben ne a ranar 13 ga watan Numbar 2024.

Wata ƙungiyar kare hakkin dan Adam ta ce zuwa yanzu alkaluman waɗanda suka mutu a rikicin da ya fara tun 21 ga watan Okotoba zuwa yanzu, ya kai aƙalla mutum 47.

KU KARANTA: Shugaban Nijar Bazoum Ya Taya Bola Tinubu Murnar Cin Zaɓe

Ƙungiyar ta ce ƴan sanda sun harbe masu zanga-zanga a lardin Namicopo da ke birnin Nampula wanda ya kasance birnin mafi yawan jama’a a kasar.

Rahotanni sun ce kashe mutanen ya sa mazauna Namicopo fara farautar ƴan sandan da ake zargi da aikata kisan.

Lamarin ya kai ga jikkata wani jami’in ɗan sanda ɗaya.

Rahotanni sun bayyana cewa dubban mutane ne suka fita kan titunan birane da kuma garuruwa don yin Alla-wadai da zargin tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 9 ga watan Oktoba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *