• Sat. Jul 12th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Gaskiya Ita ce Babbar Siffar Mumini — Barista Dan-almajiri

BySani Magaji Garko

Nov 23, 2024

DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

Babbar siffar mumini ita ce ‘Gaskiya,’ don haka duk musulmi na kwarai yakamata ya guji furta karya a cikin kalamansa domin samun tsira a gobe kiyama.

Daya daga cikin fitattun malaman Addinin Musulunci a jihar Kano dake Arewacin Nigeriya Barrista Habibu Dan-almajiri Fagge ne ya bayyana hakan cikin hudubar sallar juma’a da ya gabatar a ranar juma’ar da ta gabata.

KU KARANTA: Ku Tsara Iyali Dai-dai Yadda Zaku Iya Daukar Nauyinsu — Barista Dan-almajiri

Dan àlmajiri ya ce an rawaito Annabi sallallahu Alaihi wasalam yana cewa da wani daga cikin sahabbansa ku guji furta kalaman karya ko da ga yayanku ne, domin karya saba da jin abinda bana gaskiya ba daga bakinku saboda karya abace mai muni.

Haka kuma annabi sallallahu Alaihi wasalam wata rana ya ce da sahabbansa waye zai kame bakinsa daga barin furta kalaman karya acikin rayuwarsa zan lamunce masa shiga Aljannah, wanda hakan yana nuna mihimmanci da gaskiya take dashi a duniya da lahira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *