• Tue. Jul 15th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zamu Duba Yiwuwar Kara Alawus Din Limamai Da Ladanai — Shugaban K/H Dala

BySani Magaji Garko

Feb 4, 2025

DAGA: SANI MAI-WAYA RIJIYAR LEMO, KANO

Majalisar karamar hukumar Dala ta ce tana duba yiwuwar kara Alawus din Limamai da Ladanai a yankin domin jindadin cigaba da ilimintar da al’umma.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Surajo Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan a wani taro na musamman da limaman a sakatariyar karamar hukumar.

A lokacin taron, shugaban ya bayyana Limamai a matsayin kashin bayan cigaban al’umma.

KU KARANTA: Sanata Kawu Sumaila da Kwamishinan Yan Sandan Kano Sun Ziyarci Gurin Rikici Tsakanin Al’umma da Yan Sanda a Wudil

“Tun lokacin da na kama aiki a matsayin shugaban karamar hukumar Dala kungiyoyi daban-daban sun zo don tayani murna, amma banga kungiyar Limamai da Ladanai ba, wannan shine ya sa na gayyace ku domin naji daga bakin ku, mu ga yadda zamu inganta harkokin ku,” inji Surajo Imam.

Ya ce zasu tabbatar da bada gudun mowa don cigaban al’umma musamman masu ilimin addinin musulunci la’akari da yanayin tattalin arzikin da ake ciki.

Ya kuma bukace su da su cigaba da tabbatar da gwaji kafin daura Aure don gudun samun iyalai da basu da ingantacciyar lafiya.

A jawabinsa, shugaban Limaman masallatan juma’a na Dala Malam Nura Arzai ya yabawa shugaban karamar hukumar bisa gayyatar su da akayi inda ya ce sun dade sun jiran lokacin.

Malam Nura Arzai wanda kuma babban limaman masallacin juma’a na Mariya Sanusi Dantata dake kofar ruwa ya ce Dala tana da masallatan juma’a 34.

Ya bukaci gwamnatin yankin ta mayar da hankali kan gina Makarantun Al’qur’ani dana isilamiyya da kuma na koyan sana’o’i don cigaban al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *