• Wed. Jul 23rd, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yakin Gaza: An Cigaba Da Muyasar Firsunoni Tsakanin Isra’ila da Hamas

BySani Magaji Garko

Feb 15, 2025

Kasar Isra’ila da kungiyar sun cigaba da musayar firsunoni domin cigaban da mutunta yarjejeniyar Tsagaita Wutar kan yakin da aka kwashe sama da shekara guda anayi.

A yau, Isra’ila ta saki falasdinawa 369 da take tsare da su wanda ta kama tun bayan kaddamar da yakin, yayin da ita kuma Hamas ta saki firsunoni 3.

Motocin kungiyar bada agaji ta Red Cross ne suka karbi firsunonin Isra’ilar su uku inda ta mikawa rundunar sojan Isra’ila wanda ita ma rundunar ta tabbatar da karbar firsunonin.

KU KARANTA: Mun Yi Amfani Da Ababen Fashewa Masu Nauyin Tan 80 Don Kashe Shugaban Hezbollah — Ministan Isra’ila

Cikin wadanda Isra’ila ta saka har da mutane 29 daga Gaɓar Yamma da kogin Jordan da kuma 7 daga Birnin Kudus.

Rahotoni sun ce tuni aka fitar da mutane 24 daga cikinsu zuwa ƙasashen waje, kamar yadda ƙungiyar fursunonin Falasɗinawa ta bayyana.

Haka kuma an saki mutane 333 da aka tsare a Gaza tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023, a cewar ƙungiyar.

Daga cikin Falasɗinawa da aka saki har da waɗanda ake tsare da su bayan samunsu da laifin munanan hare-hare kan Isra’ilawa.

A nata bangaren, kungiyar Hamas ta ce ta hanyar Sulhu ne kadai za’a iya tseratar da mutane da suke hanunta ba yin amfani da karfin tuwo ba da Isra’ila da kuma kasar Amurka ke tunanin cigaba da yi.

A wata Sanarwa da Hamas ta fitar a yau, ta ce sakin Isra’ilawan da ta yi a yau, ya nuna cewa babu hanyar da za su kuɓuta ”in ba ta hanyar sulhu tare da aiki da sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta ba”.

Ƙungiyar ta kara da cewa: ”muna faɗa wa duniya cewa babu wata ƙaura, in ba ta Birnin Ƙudus ba,” a wani martani ga shawarar shugaban Amurka Donald Trump na kwashe duka al’ummar Gaza daga yankin domin mayar da su ƙasashe makwabta.

A kwanakin baya-bayan nan dai an shiga ruɗani dangane da ci gaba da aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar, bayan da Hamas ta yi barazanar dakatar da sakin Isra’ilawan, saboda zargin Isra’ila da saɓa wa yarjejeniyar, zargin da Isra’ilar ta musanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *