Aƙalla mutane biyar (5) ne aka tabbatar da rasuwarsu daga cikin mutane 15 da suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a Jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa fashewar bam ɗin ya haddasa firgici a yankin da lamarin ya faru, inda jami’an tsaro da na agajin gaggawa suka garzaya wajen don kai ɗauki.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce fashewar na iya kasancewa bam ɗin da sojoji suke yin jigilarsa ne wanda aka yi sakaci ya fashe.
KU KARANTA: Daukar Nauyin Yan Daba a Kano: Zamu Kai Sarki Muhammadu Sanusi II Kara Kotu — Barista S.S. Umar
Lamarin dai ya faru ne a titin ratse na gabashin Kano wato “Eastern bypass.”
“Na samu kiran gaggawa cewa wani abu mai tayar da hankali ya faru. Da na isa wajen, sai na ga abin kamar bama-baman sojoji ne suka fashe.
“Mutane 15 sun jikkata, kuma abin takaici, guda biyar sun rasu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa yankin domin samun kulawa ta gaggawa.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ce ɗauke da kayan fashewar, wadda ta ke kan hanyar zuwa Jihar Yobe.
Har yanzu jami’an tsaro ba su tabbatar da ko motar sojoji ce ke ɗauke da kayan fashewar ba.
Rundunar na ci gaba da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma abin da ya haddasa fashewar abun.
Kwamishinan ya roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu.