Shugaban kamfanin Gine Gine na sky Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai khadimun Nabiyyi ya bayyana Alhini da jimamin sa kan rasuwar dattijon arziki kuma hamshakin ɗan kasuwa Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.
Cikin saƙon ta’aziyyarsa, khadimun Nabiyyi ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ƙima wanda ya taka rawar gani wajen habɓaka tattalin arziki, bunkasa ilimi, da kuma samar da ayyukan jin ƙai a ƙasar nan.
Cikin wata sanarwa da Kamalu Yakubu Ali ya sanyawa hanu, SKY ya bayyana cewa rayuwar Dantata tana cike da hidimtawa al’umma da kuma kyawawan dabi’u abun koyi ga kowa.
KU KARANTA: Mutane 5 Sun Rasu, 15 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Bom a Kano
“Alhaji Aminu Dantata mutum ne da ya sadaukar da dukiyarsa da lokacinsa wajen tallafa alumma, musamman marasa ƙarfi, kuma ya kasance shugaba abin koyi ga matasa da sauran alumma.
Ya ƙara da cewa marigayin ya bar babban gibi da zai ɗau lokaci kafin a cike shi, amma abubuwan alheri da ya gudanar a lokacin rayuwarsa za su ci gaba da haskaka tunanin al’ummar Jihar Kano da ma kasa baki daya.
Khadimun Nabiyyi ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, da al’ummar Jihar Kano da kuma dukkan ‘yan Najeriya baki daya, yana roƙon Allah Madaukakin Sarki da Ya jikansa da rahama Ya kuma baiwa danginsa haƙurin jure wannan babban rashi.
Ya kuma yi fatan Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa Aljannah Firdausi ce makomarsa da sauran alummar musulmi baki daya.