Kasar Amurka ta Sanya sabon Haraji kaso 15 cikin 100 kan kayan da ake sarrafawa daga Nigeriya da kuma mabanbantan kaso kan kayayyakin wasu kasashen Afirka 12 wanda ake shigar da su Amurka.
Wannan matakin na kunshe ne cikin wata sabuwar Dokar Zartarwa da Fadar White House ta fitar a ranar Alhamis, mai taken: “Kara Sauya Yadda Ake Biyan Haraji Bisa Ka’idojin Musayar Kaya.”
Kasashen Afirka da Karin harajin ya shafa sun hada da Zimbabwe, Uganda, Mozambique, Mauritius, Ghana, Malawi, Lesotho, Madagascar da kuma South Africa.
KU KARANTA: Yakin Isra’ila da Iran: Trump Na Kokarin Yin Kuskuren Da Tsohon Shugaban Amurka Bushi Ya Yi’
Haka kuma, Amurka ta ƙara wa kayayyakin Afirka ta Kudu da ake shiga da su ƙasarta harajin kashi 30 cikin 100.
Dangantaka tsakanin Mista Trump da Shugaban Afirka ta Kudun Cyril Ramaphosa ta taɓarɓare a cikin ‘yan watannin nan.
Shugaban Amurka ya dakatar da dukkan tallafi kan Afirka ta Kudu, bisa zargin nuna wariya kan fararen fata tsiraru.
Amurka ta kuma rage haraji kan kayayyakin ƙasar Lesotho daga kashi 50 cikin 100 zuwa kashi 15, wani abu da ka iya taimakawa wajen tsare kamfanonin tufafi.