• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Muna Fatan Zaka Inganta Samar Da Tallafin Karatu A Kano — Tsofaffun Daliban Jami’ar Northwest

BySani Magaji Garko

Aug 8, 2025

DAGA: ZULAIHAT AHMED UBA, KANO

Bawa dalibai tallafi a bangaren karatunsu a lokacin da suke karatu Yana Kara musu kaimi da kwarin guiwa wajen mayar da hankali a kan karatun da suke yi.

An bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar taya murna da abokan karatun babban sakataren hukumar bada tallafin karatu ta jihar Kano, Hamisu Musa Gambo Danzaki, suka Kai masa domin taya shi murna nada Shi a matsayin babban sakatare hukumar da gwamna Abba Kabir Yusuf yayi.

Tawagar bisa jagorancin shugaban tsangayar Nazarin halayyar Dan Adam na jamiar Northwest Dr Yusuf Ahmad Gwarzo, sun Kai masa masa ziyarar ne a ofishinsa dake hukumar.

KU KARANTA: Tsofaffun Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Barranta Kansu Da Maganganun Shugaban APC Kano Abdullahi Abbas

Dr Gwarzo Ya bayyana nadin Danzaki a matsayin abinda ya dace domin an ajiye kwarya a gurbinta, duba da irin jajirjewa da sadaukarwa da Sabon babban sakatare hukumar yake da ita.

Dr Gwarzo ya bukaci Sabon babban sakataren hukumar bada tallafin karatun da yayi duk me yiyiwa don ganin bai bawa gwamna kunya ba, wajen yin aiki tukuru don ganin daliban sun samu duk damarmakin da ya kamata su samu na tallafin karatun, duba da Yadda gwamna ya maida hankali wajen ci gaban ilimi a jihar Kano .
A nasa jawabin shugaban hukumar bada tallafin karatu ta jihar Kano, Musa Danzaki ya bayyana Nasarar da ya samu da cewa ta samo asali daga hadin Kai da kwarin guiwar da abokan karatunsa suke ba Shi a ko yaushe.

Danzaki yace zai yi duk me yiwuwa don ganin hukumarsa ta yi abinda ya dace wajen bawa daliban jihar Kano tallafin karatu. Domin ya cika burin da gwamna Abba Kabir Yusuf yake dashi wajen ganin bangaren ilimi a jihar nan Yana samun ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *