• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Rano

BySani Magaji Garko

Aug 13, 2025

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Rano Muhammad Naziru Ya’u daga kujerar sa, na tsawon watanni uku, sakamakon korafin da Kansiloli 9 daga cikin 10 na karamar hukumar suka shigar a gabanta.

Kansilolin sun zargi Naziru Ya’u da rashin kwarewar aiki da almundahana wajen sayar da takin zamanin da gwamnatin jihar Kano ta tura yankin.

Da yake bayyana matakin dakatarwar, Shugabam masu rinjaye kuma mai rikon mukamin kwamitin karbar korafe-korafe na majalisar Lawan Husaini Dala, ya ce majalisar ta dauki matakin ne don tantance gaskiyar matsalolin da suke Jibge a gabanta masu alaka da shugaban.

KU KARANTA: Muna Fatan Zaka Inganta Samar Da Tallafin Karatu A Kano — Tsofaffun Daliban Jami’ar Northwest

A cewar Dala, kwamitin majalisar ya gudanar da zama na musamman da kansilolin 9 da suka yi korafin tare da sauraren bangaren su, daga bisani kwamitin ya gayyaci Shugaban shima suka tattauna da shi.

Shugaban masu rinjayen ya ce wanda ake zargi ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa, lamarin da ya sanyawa majalisar dakatar shi domin tayi binciken kwakwaf kasancewar gamsuwa da kwamitin yayi cewar akwai abubuwan da suke bukatar taza da tsifa domin fito da gaskiya.

Dala ya ce majalisar tayi amfani da ikon da doka ta sahale mata ne wajen gudanar da bincike akan shugaban, inda ya kara da cewa daga cikin zargin da ake masa har da batun rushe Kasuwar Rano da yin gaban kan sa wajen siyar da ita a farashi mai matukar tsada.

Majalisar ta bawa ma’aikatar kananan hukumomi shawarar ta mika ragamar tafiyar da karamar hukumar ga hannun mataiumakin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *