• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Muna Neman Tallafin Gwamnatin Katsina Saboda Lalacewar Hanyarmu ta Kandawa — Al’ummar Batsari

BySani Magaji Garko

Aug 15, 2025

Al’umma garin Kandawa dake karamar hukumar Batsari a jihar Katsina sun bukaci gwamnatin jihar data kai musu dauki domin gyaran hanyar shiga garin wacce ta lalace.

Wani dan asalin yankin Malam Mubarak Basiru Kandawa ne ya yi kiran a yayin zantawarsa da ‘yan Jaridu.

Ya ce hanyar mai tsawon kilomita talatin (30) na bukatar daukin gaggawa duba da yanayin da take ciki.

KU KARANTA: Gawar Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Isa Katsina

Mubarak Basiru Kandawa ya ce garin na da dumbun al’umma wanda akasarin su manoma ne.

Ya kuma bayyana cewa ana noman Kankana da Dandakali da Albasa da Shinkafa da kuma Rake.

Ya ce harkokinsu suna komawa baya gami da fuskantar tasgaro sakamakon rashin hanya harkokin kula da lafiya na cikin barazana musamman ga mata masu juna biyu da Sauran marasa lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *