An kone wata mota wacce ake tunanin ta ‘yan sanda ce a caji ofis din rundunar ƴan sanda ta kasa reshen karamar hukumar Garko dake Jihar Kano ne Sakamakon arangama tsakanin Jami’an tsaro da ‘yan sandan yankin.
Rahotanni sun ce lamarin ya samo asalin ne sakamakon dagewa da masu haya da babura (‘yan Acaba) da sauran al’ummar gari su ka yi na dole sai an fito musu da wasu da ake zargin barayin babur ne sun kashe su.
Wani mazaunin garin da bai so a ambaci sunansa ya gayawa GLOBAL TRACKER cewa an kamo mutanen da ake zargi sun Kashe Dan acaban ne bayan da suka sassara shi gami da yin awun gaba da babur Dinsa kirar Bajaj ta hanyar bibiyar wayar wanda aka kashe.
“Su wannan mutane ana zarginsu da tare wani Umar Idris Dan kauyen Kamfa a karamar hukumar ta Garko, suka kwace masa Babur kafin kazo tashar ilalu bayan ya dawo daga garin Buda, suka kuma kashe shi ranar larabar da ta gabata, to bayan an bibiyi wayarsa aka kama mutane biyu da ake zargi ciki harda Dan uwan Marigayin, Bayan an kama su ne abokan sana’ar Marigayin Umar da sauran al’umma suka dage dole sai an fito musu da wadanda ake zargi suma su kashe su, lamarin da ya janyo fito-na-fito tsakanin ‘yan sanda da Al’ummar Gari,” inji Majiyar.
Wata majiyar ta tabbatar wa da GLOBAL TRACKER cewa an kone motar, Amma baza ta iya tantance ko motar ‘yan sanda ba ce ko kuma wasu daga cikin motocin da aka Ajiye a ofis ba ne.
Bayanan da wannan jaridar ta tattaro sun ce yanzu abubuwa sun lafa saboda an sake tura karin ‘yan sandan kwantar da tarzoma wato “MOPOL” domin maido da Doka da oda a yankin.
To Amma Jaridar GLOBAL TRACKER ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya ce yana cigaba da tattauna bayanai yadda lamarin ya kasance.