• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kungiyar CSADI Ta Tallafawa Mata da Yara 200 Da Abinci Mai Gina Jiki a Kano

BySani Magaji Garko

Sep 14, 2025

Kungiyar tallafawa Marayu da masu karamin karfi da ma Mata wato CSADI ta tallafawa mata da kananan Yara 200 da ingantaccen abinci mai gina Jiki da kuma dabarun hada shi don yaki da cutar Tamowa da kuma inganta rayuwar iyali.

Shugabar Kungiyar Hajiya Zainab Ahmad Suleiman ce ta jagoranci harar da matan dabarun kula da lafiyar al’umma da koya musu dabarun hada abincin da ingantacciyar hanyar shayarwa da tazarar iyali gami tsafta, horon da ya gudana a Kauyen San-San a karamar hukumar Danbatta dake Kano.

A cewarta, duk da ire-iren kayan abinci da ake Nomawa a Yankunan karkara, ana samun yara da mata da suke fama da yunwa sakamakon karancin abinci mai gina jiki, inda ta ce hada sinadaran da suka da ce zai taimaka wajen samar da sinadaran da jikin mutum yake bukata don aiwatar da harkokin yau da kullum cikin koshin lafiya.

KU KARANTA: DA DUMI DUMI: KANO; An Kone Motar Yan Sanda Sakamakon Yunkurin Kashe Barayin Babur Da Suka Kashe Dan Acaba a Garko

Dangane da kididdigar da Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin Duniya UNICEF ya bayar na karuwa yara da ka iya rasa ransu sakamakon karanci abinci mai gina jiki a Nigeriya kuma, shugabar ta CSADI ta ce zasu kara zage damtse domin ganin sun cigaba da tallafawa mata da Yara don samun abinci mai gina jiki da nufin yaki da kananan cututtukan da suke damun al’umma.

“A yau mun tallafawa mata da Yara 200 da abinci mai gina jiki guda 400, kowacce uwa mun bata guda biyu ita da taron ta, mun kuma koya musu yadda za’a hada Wannan sinadari, munyi hakan ne don tallafa musu su sami abinci mai gina jiki, kuma hakan zai taimaka wajen yaki da cutar Tamowa,” inji shugabar.

“Dama muna tallafawa mata da kananan Yara, to wata sanarwa da kididdiga da UNICEF ta fitar ya dame mu matuka, shine yasa muka Kara jajircewa, kuma insha Allah zamu cigaba da tallafa musu, muna fatan gwamnatoci zasu jajirce don samawa mata da yara ingantaccen abinci mai gina jiki,” inji Zainab Suleiman.

A jawabinsa, Dagacin garin San-San Ibrahim Babangida yabawa kungiyar yayi bisa tallafawa mata da yaran yankin yana mai cewa horon da aka bawa matan zai taimaka wajen kula da lafiyar al’umma.

Babangida ya kuma ce shi da sauran magidantan yankin za su yi kokarin Dabbaka horon da aka yi musu don rage kashe kudade wajen siyan magani.

Samira Yusuf da Hafsa Isa da kuma Ramatu Rabi’u Yusuf na daga cikin matan yankin da suka amfana da koyon dabarun hada abinci mai gina jiki musamman don kula da lafiyar su da ta ‘ya’yan su, sun kuma bada tabbacin aiki tukuru gami da tallafawa mazajen su don samar da abinci mai lafiya a gidajen su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *