• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

RA’AYI: Shin Malam Lawan Triumph Batanci Ya Yi Ga Annabi ? — ABUBAKAR MURTALA IBRAHIM

BySani Magaji Garko

Sep 28, 2025

Ban cika son tsoma baki na a kan komai ba amma zan yi magana a kan batun Malam Lawan Triumph saboda al’amari ne da ya shafi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam.

Na saurari cikakken bidiyon da aka fitar wanda ya yi wannan furuci a yayin wani karatu da ya gabatar, a fahimtata da kuma yadda na kalli kalamansa da ya haifar da ruɗani.

A fahimtata da Malam duk da cewa ban taɓa mu’amala da shi ba, daga yadda na ke kallo ko sauraron karatunsa na ke fahimtar kamar mutum ne mai fushi da izza da kuma ɗaukar zafi, ba lallai fahimtata ta zama gaskiya ba saboda na ce ban yi mu’amala da shi ba.

KU KARANTA: Kungiyar CSADI Ta Tallafawa Mata da Yara 200 Da Abinci Mai Gina Jiki a Kano

Ban gamsu cewa a hankalinsa da iliminsa zai yi ɓatanci ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ba ko da kuwa a magagin bacci ya ke ba.

Sai dai abinda ya buga misali da shi a yayin karatun da ya gabatar a iya cewa tsantsar rashin ladabi ne kuma kuskure ne babba.

Me ya sa na ce haka?

Dalilai na a nan su ne kamar haka:- A duk lokacin da aka ce za a bayar da misali, ana kwatanta abu ne da makamancin daraja, ko dai wanda su ke daidai da daraja ɗaya, ko kuma wanda su ke kusa da daraja.

Idan kuwa ba misalin da ya shafi daraja ba ne, ba za ka kawo misalin da zai zama cin fuska ga wanda za ka bayar da misalin a kansa ba.

A baya na taɓa yin rubutu a kan malamai da kuma waɗanda ke kiran kansu malamai saboda yadda kafofin sa da zumunta na zamani su ke bai wa kowa damar yin bidiyo wasu don yaɗa ilimi, wasu domin neman suna, wasu ma don haifar da ruɗani da fitina haka siddan a tsakanin al’umma.

Taka rawar tsattsauran ra’ayi da ƙida

Da yawan lokuta zafafawa a kan aƙidar da wasu ke ɗauka ne ya ke sakawa wasu su yi furuci da bai kamata ba, kamar furucin da ke kama da zagi, ko cin mutunci ko cin zarafi wasu ma har da yankewa mutum makoma a lahira (ba tare da su sun san tasu makomar ba).

Ana samu a kowanne ɓangare daga malamai da ke da bambancin aƙida ko ra’ayi. Ko da cewar duniya ba za ta taɓa zama kan manufa guda ba dole sai an samu rarrabuwa, amma ba wai hakan na nufin mutum ya yankewa mutum makoma ko izgili ko cin zarafi ko kuma wani abu da ke kama da fasikanci ba, na kirashi da fasiƙanci saboda malamai sun karanta kuma na ji cewa zagin musulmi fasikanci ne.

Kuma rarrabuwar nan da ake yi fa an gargaɗi musulmi a kanta cewar kada mu rarrabu, kenan duk wanda ya yi abinda ya ke so sai ga abinda ba ya so. Amma saboda son zuciya na wasu ko da wani ɓangare ya zo da gaskiya sai wani ya ƙi karɓa ya kafe a kan rashin gaskiya ko da fa ya sam ba a kan gaskiya ya ke ba, wai don kada a ce an fishi hujja.

A sanina malamai da masu tsoron Allah na karbar gaskiya ko da daga bakin maƙoyinsu ne indai fa gaskiyar ce.

A fahimtata idan aka ce malami ya na nufin mutum masani da ke karantar da mutane don rayuwarsu ko dai ta duniya da kuma samun lahira. To fa wannan mutum mai daraja bai kamata a sameshi da aikata wani abu da zai iya kama da saɓawa da koyarwar da ya ke karantarwa ba.

Mu koma batun Malam Lawan, a kwanakin baya na ga gayyatar da ƴan sanda su ka yi masa a Kano wanda har su ka shawarceshi ne ko su ka gargaɗeshi don ganin ya sauya salon wa’azinsa, domin a fahimtar jami’an, kalaman da ya ke yawan yi a wurin karatunsa na haifar da ruɗani da kuma tunzura wani ɓangare wanda hakan na iya barazana ga zaman lafiya.

Ba na goyon bayan yadda wasu ke tallafa aƙidarsu yayin karantar da littafin Alkur’ani ko wani littafi na addini, karantar da abinda ka karanta a littafi matuƙar littafin sahihi ne.

Ba na goyon bayan yadda wasu ke fakewa da mumbari ka masallaci ko wa’azi wajen tallata siyasa ko ƴan takara.

Ba na goyon bayan yadda wasu ke amfani da mabiyansu don tinziri ko izgili ga wasu da su ka saɓa da ra’ayi.

Kowa a duniya ya na rayuwa ne bisa wani abu da ya yi imani da shi.

Musulmi na rayuwa ne da imanin cewar matukar ya yi addininsa da gaskiya daidai gwargwado zai shiga aljanna.

Kirista ma na rayuwarsa ne cike da yardarsa cewar matuƙar ya tsaya a kan gaskiyarsa aljanna zai shiga.

Haka kuma akwai wanda bai ma yarda da kowanne addini ba kuma rayuwa ya ke iya fahimtarsa.

Ba za ka hana wani yin abinda ya yarda da shi ba domin dokar ƙasa da aka fahimci akwai mabambanta mabiya addini da fahimta, sai ta bai wa kowa damar yin addinin da ya yarda da shi. Kamar yadda ba ka yarda a soki addininka ba, haka su ma ba za su so a soki nasu addinin ba, Allah ne ya haɗa zaman a haka.

Shawara ga gwamnati ko mahukunta

Akwai buƙatar dukkan wani da zai dinga tara mutane a wani taro ko dai na addini ko na siyasa ko ma dai wanne irin taro ne ya na da kyau a yi wani tsari da zai ƙunshi wasu sharruɗa da sai an cikasu.

1. Kamata yayi a dinga yin gwajin ƙwaƙwalwa don tabbatar da lafiyar ƙwaƙwalwar mutum
2. Gwajin shan kayan maye
3. Tabbatar da ɗabi’unsa ba shi da saurin fushi ko tunzuri ko zafi aƙida
4. Tabbatar da kalamansa ba zafafawa
5. Tabbatar da rashin tsauri wajen tunzura jama’a
6. In da hali ma a taƙaita tallafa ƙungiyanci ko wani abu a wuraren karatu ko masallatai

Sannan ya na da kyau a dinga bayar da bita a kan irin kamalan da za a dinga yi a yayin taron jama’a da za su taimaka wajen haɗin kai, zaman lafiya da tsaro.

Daga ƙarshe ina mai shawartar jama’a a kan kada bambancin aƙida ta addini ko siyasa ya sa mu dinga yin rashin adalci ba ga musulmi ba ko da kirista ne domin ya na da haƙƙi.

Kada mu sauya ma’anar zance ko furuci saboda bambancin aƙida ko fahimta.

Sannan mu kaucewa tauye haƙƙin wani saboda mun saɓa a ra’ayi.

Addinin musulunci dai zaman lafiya ya ke koyarwa, bai kamata mu dinga kiran kanmu muslmi a baki a aikace kuma mu saɓa da koyarwar addinin ba.

Allah ya sa mu dace

ABUBAKAR MURTALA IBRAHIM 
Shugaban Matashiya TV da rediyo.

Marubuci ne kuma ɗan jarida.

Mai bincike da neman Tallafin ga marasa gata.

Injiniya kuma mai ƙirƙira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *