• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

CSADI Ta Tallafawa Mata Masu Juna Biyu Da Yara 400 Da Abinci Mai Gina Jiki a Kano

BySani Magaji Garko

Sep 28, 2025

Kungiyar tallafawa Marayu da masu karamin karfi CSADI ta rabawa mata masu Juna biyu da kananan Yara su 400 da garin Bul-Bul wanda ya kasance abinci mai gina jiki da suke bukata don inganta garkuwar jikin su.

An raba kayayyakin ne Kauyen Rantan da Bebeji a karamar hukumar Bebeji da kuma karamar hukumar Kura dake nan Kano.

Daya daga cikin matsalolin da ake fuskanta musamman a Yankunan karkara shine cutar Tamowa wacce take barazana ga lafiya Yara harma da mata masu Juna biyu lamarin da ya sanya kungiyar ta CSADI ta dauki gabarar hada garin Bul-Bul don rabawa mata gami da koya musu yadda ake hada shi gami da wayar da kan iyalai don samar da abinci mai gina jiki.

KU KARANTA: Kungiyar CSADI Ta Tallafawa Mata da Yara 200 Da Abinci Mai Gina Jiki a Kano

“Duk inda muka je rabon wannan gari, Muna koyawa mata yadda zasu hada nasu da kansu, da dabarun ingantacciyar hanyar shayar da jarirai Nonon Uwa da kuma bada tazarar hauhuwa gami da dabarun kula da ciki kafin haihuwa harma da karfafa gwiwa zuwa awun ciki ga mata masu Juna biyu,” inji Hajiya Hasana, daya daga cikin jami’an rabon kayayyakin.

“Dukkan matan da suka amfana, muna nuna musu dabarun kula da lafiya da kuma bada shawarwari musamman ga matan da suka fito daga karkara sakamakon wasu daga cikin su suna da karancin Ilimin Zamani da kwarewa a wajen dabarun sarrafa Abinci mai gina jiki,” inji ta.

A tattaunawarsa da GLOBAL TRACKER, Sarkin Fulanin karamar hukumar Bebeji Adamu Umar Adamu ya ce tallafin ya zo dai-dai lokacin da ake bukatar sa la’akari da yunwa da ake fama da ita duk kuwa da lokacin kaka da ake ciki.

Adamu Umar wanda kuma shine dagacin Bebeji ya godewa kungiyar inda ya bukaci kungiyoyin al’umma da su rika daukar ire-iren wadannan matakai da za su inganta rayuwar iyali.

“A wasu lokutan zaka ga ba’a yaye wani ba, an sami cikin wani yaron, to a irin wannan lokacin ana bukatar samar da abinci mai gina jiki sosai ga ita uwa da ma jarirai, akan wannan dole ne hankalin Magidanci ya koma bibiyar halin da iyalinsa yake ciki,” inji Sarkin Fulani.

Ya kuma bukaci gwamnatoci da masu rike da madafun Iko harma da mawadata da su rika tallafawa tsarin kula da lafiyar mata masu Juna biyu da kananan Yara a Bebeji da ma Jihar Kano baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *