• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Matsalar Tsaro Ce Ke Kokarin Kawo Ƙarshen Noman Ridi a Arewacin Nigeriya — Danliti Y.Y Dawanau

BySani Magaji Garko

Oct 3, 2025

DAGA: NURA GARBA JIBRIN, KANO

Kungiyar ‘yan Kasuwa da masu safarar Ridi ta kasa reshen Jihar Kano ta bayyana cewa matsalar tsaro na barazanar kawo ƙarshen Noman Ridi a Arewacin Nigeriya.

Shugabar kungiyar a nan Kano dake kasuwar Dawanau Ibrahim Muhammad Dawanau wanda aka fi sani da Danliti Y.Y ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da GLOBAL TRACKER.

Ya ce matsalar tsaro dake damun jihohin Borno da Zamfara da Katsina da Sokoto da Yobe shine ke barazanar kawo ƙarshen Noman Ridi, inda ya ce akwai bukatar mahukata su dauki matakin da ya dace don kawo ƙarshen matsalar.

KU KARANTA: Manoma Na Fargabar Cigaba Da Asara Sakamakon Karancin Ruwa a Kano

Danliti Y.Y ya kuma ce baya ga tsaro, karancin kayan aiki, kama daga Taraktocin Noma da Ingantaccen Iri da magungunan kashe kwari wasu ne daga cikin abubuwan da ke damun Manoman Ridi a Arewacin kasar nan.

“Yanzu idan da za’a samu Takin Zamani dai saukin farashin da Taraktocin Noma da Ingantaccen Iri da magungunan kashe kwari, to wallahi ni kadai zan iya Noma Hekta 100, amma a yanzu ko Hekta 30 bazan iya Nomawa ba,” inji Danliti.

Shugaban ya bukaci gwamnatoci tarayya da na jihohi da kananan hukumomi da dukkan masu ruwa da tsaki da su dauki matakin da ya dace don kawo ƙarshen matsalar.

A jawabinsa, matemakin shugaban kungiyar Babangida Mansur ya yabawa gwamnatin Jihar Kano musamman kwamishinan Kasuwanci kan yadda yake daukar matakan da suka dace don cigaban ‘yan Kasuwar ta Dawanau.

Mansur ya ce akwai bukatar gwamnatin Jihar Kano ta dauki gabarar Horar da Yan kasuwa dabarun karbar bashin da gwamnatin tarayya da ma kungiyoyin Duniya ke baiwa Yan kasuwa.

Acewarsa matukar gwamnati ya dauki matakin samarwa da Yan kasuwa Jarin da babu kudin ruwa a cikinsa hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Jihar Kano da samar da kudaden shiga gami samar da aikin yi.

Ya kuma bukaci kungiyoyin Yan kasuwa da su hada kansu domin samar da hanyoyin da zasu kawowa kansu cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *