Kungiyar tallafawa Marayu da masu karamin karfi CSADI ta tallafawa mata masu Juna biyu da kananan yara sama da 600 da abinci mai gina jiki don yaki da cutar yunwa da kuma tsumburewar kananan yara musamman a yankunan karkara a Jihar Kano.
CSADI ta kuma harar da matan da ma magidanta yadda ake hada abincin da yadda ake hada Sabulu da nufin bunkasa rayuwar mata da kananan yara a karamar hukumar Bebeji dake Kano.
Hajiya Zainab Ahmad Suleiman, shugaban kungiyar ce ta bayyana hakan a tattaunawarta da GLOBAL TRACKER bayan kammala horon gami da rabawa matan abincin da nufin kula da lafiyar su da bunkasa tattalin arzikin mata a yankunan karkara, taron wanda aka gudanar a karamar hukumar Bebeji a Alhamis din nan.
KU KARANTA: Kungiyar CSADI Ta Tallafawa Mata da Yara 200 Da Abinci Mai Gina Jiki a Kano
Shugabar ta ce a watanni baya ta yi aiki da gidauniyar Dangote wanda suka rika tallafawa mata da yara a Bebeji, to amma da gidauniyar ta dakatar da aikin da kuma tsakanin bukatar da ake sai ta dauki gabarar tallafawa matan da kanta domin kula da lafiyar al’umma da kuma tallafawa masu karamin karfi wanda CSADI ta dade tana tallafawa.
“Mun tallafawa mata sama da 600 da garin Bul-Bul din nan wanda hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta amince da shi, kuma alhamdulillah su da kansu sun gani cewa abinda suke Nomawa a yankunan su, sune muke hadawa, sun karba sunji dadinsa,” inji shugabar.
“A wannan lokacin mun koya musu yadda ake hada Sabulu, Sabulun wanka da na wanki da Sabulun wanke Gashi, mun kuma koya musu yadda ake hada wanna kunu mai matukar tasiri ga lafiyarsu saboda idan kana ta fada musu da baki baza su gane ba, kuma idan suka hada shi ba dai-dai ba zai iya zamar musu illa, shine yasa muka nuna musu yadda ake hadawa da sarrafawa a aikace,” inji Zainab Suleiman.
Ta kuma bukaci gwamnatoci da ‘yan Siyasa da Shugabannin Al’umma da su dauki gabarar tallafawa mata da kananan yara kasancwarsu masu rauni a cikin al’umma.
Lokacin da yake karbar ayarin CSADI, Hakimin Bebeji Alhaji Sarki Yusuf Bayero, wanda shine Yandakan Kano ya bayyana farin cikinsa bisa yadda kungiyar ta dauki gabarar tallafawa matan yankin duk kuwa da dakatar da aikin da gidauniyar Dangote ta yi.
Ya kuma bada tabbacin yin aiki yin aiki da kungiyar don cigaban al’ummar yankin, inda ya ce masarautar Kano da ma ta yankin za su yi duk mai yuwuwa da samun nasarar aikin.
Shima Sarkin Fulanin Bebeji kuma Dagacin garin ya ce tallafin da kungiyar ta kai ya zo dai-dai a lokacin da ake bukata la’akari da adadin yara da mata da suke siradin kamuwa da cutar yunwa.
Ya shawarci magidanta da su cigaba da jajircewa da kula da cimakar iyalansu don farin cikinsu da inga lafiyarsu.
Hassana Jibrin dake kofar Kudu, Bebeji da Jamila Ibrahim sun yabawa kungiyar inda suka bada tabbacin cigaba da haka kayan don kula da lafiyarsu.