Kungiyar tallafawa Marayu da masu karamin karfi CSADI ta gudanar da gangamin tallafawa mata masu Juna biyu da kananan yara yadda zasu yaki cutar Tamowa da tallafawa mata sama da 200 yadda zasu hada abincin mai gina jiki don kawo ƙarshen matsalar.
Kungiyar ta kuma duba yadda ake cigaba da aikin rigakafin cutar Polio garin San-San da garin Danbatta dukka a yankin karamar hukumar Danbatta.
Shugabar kungiyar ta CSADI Hajiya Zainab Ahmad Suleiman MFR, JP wacce ta jagoranci aikin ta ce tallafin yana daga yunkurin kungiyar don yaki da Tamowa da ma sauran cututtuka da suke damun kananan yara musamman a yankunan karkara a Jihar Kano.
KU KARANTA: KANO: CSADI Ta Rabawa Mata Masu Juna Biyu Da Yara 300 Abinci Mai Gina Jiki a Bebeji
“Muna gabatar da wannan shiri na tallafawa mata a yankuna daban-daban musamman a karamar hukumar Bebeji da Kiru da Kura da Danbatta dama Madobi, dukkan wannan tallafin da nake yi da kudi na nake yi, mun san cewa akwai kananan yara da suke da cutar Tamowa, kuma matukar ana son yaki da wannan matsala dole ne sai an wayar da kan iyaye mata da Maza, sannan sai an basu wani tallafi da zasu ga abun a aikace,” inji Hajiya Zainab Suleiman.
“Dukkan abun da muke hadawa a wannan garin Bul-Bul da yake yaki da wannan cuta abubuwa ne da akwai su a karkara, so muna rokon iyaye Maza su rika bawa mata ire-iren wadannan sinadarai da zasu inganta lafiyar iyalunsu domin idan sun sami ire-iren wadannan sinadarai suna matukar rage yawan kashe kudi don neman lafiya a asibiti,” inji Zainab.
A jawabinsa Dagacin garin San-San a karamar hukumar Danbatta Ibrahim Babangida yabawa CSADI ya yi bisa yadda take tallafawa da kuma wayar da kan jama’a a yankin.
“Gaskiyar magana a harkar rigakafi bamu da wata matsala, dukkan magidanta suna fito da yaransu domin ayi musu digon Polio, idan kuma an sami wani magidanci da yaki karba, muna kokarin wayar da kansa, mu nuna masa misali a aikace, hakan ne ya sa ba’a taba samun wani yaki amincewa ayi wa ‘ya’yansa ba,” inji Ibrahim.
A jawabinsa, Badamasi Umar shugaban kungiyar cigaban yankin “San-San Ina Mafita ?” ya yi kira ga mahukunta a Danbatta da su tallafa tare da kai musu jami’an lafiya da zasu rika aikin kwana a asibitin yankin yana mai cewa wata kungiya ‘IMPACT’ da gyara gami da daga darajar asibitin yankin amma basa samun likitan da zaiyi aikin kwana don kula da marassa lafiya.
Ya ce mutanen kauyuka guda 8 ne ke zuwa asibitin wanda suka hadar da Kanwaye da Kwasauri da Baro da Zago da Dungu da Gajaja da Kagadama da kuma Gasakori.
Shugaban na San-San Ina Mafita ya roki mahukunta a Danbatta da su tallafa musu don kawo ƙarshen matsalar da suke fama da ita.