DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na biyu karkashin jagorancin Hakimin karamar hukumar Tarauni Alhaji Bello Ado Bayero ya amince da nadin Alhaji Abdullah Bello Gaya P.A a matsayin mai-unguwar Hotoro GRA, duba da irin gudunmawa da yake baiwa alumma yankin ta bangarori da dama.
Alhaji Bello Ado Bayero ya bayyana Alhaji Abdullah P.A a matsayin matsakaicin dattijo, dake kokarin ganin ya tallafawa rayuwar matasa dake yankin domin ganin sun amfani kansu da sauran al’umma baki daya.
Hakan ne yasa aka nada shi mukamin na mai unguwar Hotoro GRA domin kara masa karfin gwiwar aiwatar da ayyukan alheri ga alumma.
KU KARANTA: CSADI Ta Yi Gangamin Wayar Da Kan Mata Kusan 200, Da Yaki da Cutar Tamowa, Duba Aikin Polio a Kano
An haifi Alhaji Abdullah Bello Gaya a unguwar Tudun wuzurci dake cikin Birnin Kano a shekarar 1972.
Yayi karatunsa na primary a makarantar Gidan makama 1 1979 daga nan ya tafi babbar sikandire dake Gwale, ya samu Babbar diploma a kan harkokin Akanta da gudanarwa a makarantar kimiyya da fasaha dake Kano wato Kano state Polytechnic inda yake da mace Daya da kuma ‘ya’ya 9.
Shima anasa jawabin mai garin Hotoro Alhaji mustapha Abubakar ya bayyana farin cikinsa mutuka da nadin, inda yace hakika an dora kwarya a gurbinta.
Taron ya samu halartar alumma da dama suka hadarda limamai, yan kasuwa da sauran shugaban alumma.