• Mon. Jul 7th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Wasu Mutane Na Shirin Tayar Da Hankali A Lokacin Zaben Gwamnoni — DSS

ByGlobal Tracker

Mar 9, 2023

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce akwai shirin da wasu mutane ke yi na tayar da hankali a wasu sassan Nigeria a zaɓen gwamnoni da ke tafe.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ya fitar, ta gargaɗi mutane ko kungiyoyi da su guji yin duk abin da zai tayar da hankali domin kauce wa fushin hukumar da sauran jami’an tsaron Nigeria.

A don haka DSS ɗin ta ja kunnen ‘yan siyasa da su zama masu bin doka da oda a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke shirin fita rumfunan zaɓe domin zaɓen gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki a ranar 18 ga watan Maris.

KU KARANTA: Bawa NHFSS Damar Samar Da Tsaro a Lokacin Zabe Zai Kara Mana Karfin Gwiwa — Abdullahi Al-ameen

Hukumar ta ce a shirye ta ke domin kare ‘yan Nigeria waɗanda ke da niyyar fita kaɗa kuri’a.

DSS ɗin ta kuma ce ta shirya tsaf tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro wajen dakile duk wani yunkuri na kawo tashin hankali a lokacin zaɓen.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *