Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya sake samun nasarar komawa wa’adi na biyu na mulkin jihar, bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamna da aka gudanar a ransar Asabar ɗin da ta gabata.
INEC ce ta bayyana ɗan takara a matsayin wanda ya lashe zaɓen a Maiduguri babban birnin jihar a ranar Litinin.
KU KARANTA: APC Na Dab Da Lashe Zaben Gwamna a Jigawa
Zulum ya lashe zaɓen ne da ƙuri’a 545,542 sai kuma jam’iyyar PDP ta ke da ƙuri’u 82,147.
Jam’iyyar LP wadda ta taka rawar gani a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabirairu ta zo ta uku da kuri’a 1,517.
BBC Hausa