• Wed. Jul 16th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Majalisar Dokokin Kano Ta Gamsu Da Yadda Aikin Kwashe Shara Ke Gudana

ByGlobal Tracker

Jul 17, 2023

Majalisar dokokin jihar Kano ta bayyana gamsuwar ta bisa yadda aikin kwashe shara yake gudana a fadin jihar nan.

Shugaban Majalisar Rt Honarabil Isma’il Jibrin Falgore ne ya bayyana hakan lokacin da tawagarsa ta gamu da ma’aikatan hukumar kwashe shara da tsaftar Muhalli ta jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Ahmadu Haruna Zago a unguwar ja’in.

KU KARANTA: Zamu Samar Da Tsarin Tsaftace Kasuwannin Kano — Dan-zago

KU KARANTA: Zu Mu Samar Da Tsarin Yaki Da Zubar Da Shara Barkatai a Kano — Dan-Zago

Jibrin Falgore ya ce duba da yadda Dan zago yake gudanar da aikinsa tun bayan daya karbi hukumar wajen tsaftace birnin jihar Kano da kewayen ta, ya zama wajibi a Yaba masa domin Kara masa kaimi wajen tafiyar da hukumar.

Da yake nasa jawabin tun da farko, shugaban hukumar Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya ce aikin da hukumar sa take gabatarwa abu ne daya zama matukar anasan cigaban Kano tare da bukatar ‘yan majalisaun jihar nan dasu bayyanawa hukumarsa duk Wani abu Wanda suke ganin hukumar tasa ta kaucewa ka’ida domin gyarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *