Allah ya yiwa Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi Bayero rasuwa.
Daya daga cikin Iyalansa ne ya shaidawa DW Hausa cewa nan gaba kadan za’a sanar da lokacin jana’izarsa.
Alhaji Abbas Sunusi kawu ne ga Sarkin Kano Muhamamd Sunusi II, kuma mahaifi ga shugaban jamiyyar APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas.
Marigayin shi ne Wamban Kano babban dan majalisar Sarki kafin daga likkafar sarautarsa zuwa Galadiman Kano.