• Sat. Apr 18th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Shaik Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi Ya Rasu

BySani Magaji Garko

Apr 4, 2025

Sanannen malamin addinin musulunci a Nigeriya Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya rasu.

Shaik Ibrahim Disina, daya daga cikin manyan malamai a Nigeriya kuma darakta janar na gidan talabijin na “Sunnah TV” ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Ya ce Shaik Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya rasu ne bayan doguwar jinya.

KU KARANTA: Galadiman Kano Abbas Sanusi Ya Rasu

GLOBAL TRACKER ta samu labarin cewa ko a sallar idin da ta gabata ta karamar Sallah ba’a ga Dutsen Tanshi ba a Masallacin da yake jagorantar Sallah, lamarin da ya Kara fito da yanayin rashin lafiyar da malamin dan asalin Jihar Bauchi yake fama da ita.

Ga abinda da Shaik Disina ya wallafa:

“Mutuwa Rigar kowa!!

“Allah ka jikan Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi.

“Allah ka kai haske kabarinsa, Ka gafarta masa kurakuransa, Ka sanya Aljannah ce makomarsa, Ka kyautata bayansa, ka bawa iyalansa dangana ameen.

“Allahu Akbar shikenan fa!!

“Allah ya hadamu gidan Aljannah.

Malamin dai yayi kaurin suna a kafafen sada zumunta na zamani wajen bada fatawowi da suke jawo ce-ce-ku-ce a Nigeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *