Dakarun Sojojin Nageria sun yi nasarar ceto matar marigayi Janar Rabe Abubakar mai ritaya daga hannun masu garkuwa da mutane yayin wani samame da suka kai kan maboyar masu aikata laifuka.
Majiyoyin soji sun bayyana cewa an samu nasarar ceton ne a yayin ci gaba da gudanar da bincike da share yankunan da ake zargin masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka ke amfani da su.
KU KARANTA: Hadin Gwiwar Sojojin Nijeriya da Faransa: Ma’anar Ziyarar Janar Charpy zuwa NDA Kaduna
Rahotanni sun ce an hada matar da iyalanta, kuma tana samun kulawar lafiya da sauran tallafin da ya dace.
Marigayi Janar Rabe Abubakar ya rasu ne yayin da matarsa ke tsare a hannun masu garkuwa, lamarin da ya jawo alhini da kira ga hukumomin tsaro su kara kaimi wajen ceto sauran wadanda ke hannun masu garkuwa a fadin kasar nan.