Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci al’umma da masu ruwa da tsaki da su Kai Korafe-korafen da suke da shi ko shawarwari game da Aiyukan Hukumar tsarawa da raya Birane ta Jihar Kano KNUPDA.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hanun sakatariyar kwamitin bincike da gwamnatin Jihar Kano ta kafa wato Rahama Malam Alhaji ta ce dukkan shawarwari ko korafe-korafen za’a rubuta su ne kai staye ga shugaban kwamitin binciken Dakta Dalhatu Aliyu Sani.
Sanarwa ta ce za’a gabatar da Korafe-korafe ne ko shawarwari game da dukkan ayyukan hukumar musamman abin da ya shafi bayar da izinin gine-gine da kula da ci gaban gine-gine, da sauran al’amuran da suka shafi dokoki da ƙa’idojin tsara birane.
KU KARANTA: Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamnan Kano Da Grandi Khadi Akan Alaƙalin Hukumar Hisba Sani Tanimu
Kwamitin na bukatar jama’a da su gabatar da ƙorafe-ƙorafe kan ko ana samun jinkirin bayar da lasisin gini da na bunƙasa muhalli da amincewar tsare-tsaren gine-gine da amfani da fili da matakan tilastawa da sashen kula da gine-gine ke ɗauka (enforcement), da kuma duk wani ƙorafi da ya shafi yadda KNUPDA ke gudanar da ayyukanta.
![]()
“Dukkan ƙorafe-ƙorafe da takardun shawarwari su kasance an rubuta su kuma an aika su zuwa ga Shugaban Kwamitin Bincike kan ayyukan hukumar KNUPDA Hon. Dalhatu Aliyu Sani, PhD, IION,” inji sanarwar.
Sanarwa ta kuma bukaci dukkan shawarwari ko korafe-korafe ya rubuta cikakken adireshinsa da Lambar waya da sauran bayanai.
“Kowanne mai ƙorafi ya tabbatar ya rubuta cikakken sunansa da lambar wayarsa da cikakken adireshinsa tare da bayyana ƙorafinsa a sarari cikin taƙaitaccen bayani. Haka kuma, idan akwai hujjojin takardu masu goyon bayan ƙorafin, a haɗo da su,” inji sanarwar.
“Za a karɓi dukkan ƙorafe-ƙorafen da takardun shawarwari a Hedikwatar hukumar KNUPDA dake kan Titin Durbin Katsina, Bompai, Kano,” inji Rahama.
Ranar rufe karɓar ƙorafe-ƙorafe da takardun shawarwari ita ce Laraba, 1 ga Yuli, 2026.
“Dukkan bayanan da za a gabatar dole ne su kasance na gaskiya da kuma cikakkiyar Hujjar mai inganci kuma an gabatar da su cikin kyakkyawar niyya,” inji shugabancin kwamitin.
Sanarwar ta kara da cewa Kwamitin na da ikon tantance sahihancin duk wani bayani da aka gabatar masa.