Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da haramta sana’ar tura fina-finai ta wayar salula, wato “Downloading”, a dukkan ƙananan hukumomin jihar 44.
Mujahid Aminundeen, Mukaddashin babban Kwamandan hukumar ne ya sanar da hakan cikin wani sakon murya da ya aikowa jaridar GLOBAL TRACKER.
A cewar sanarwa, daukar matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da hukumar ke yi na kare tarbiyyar al’umma, ɗabi’u ta gari da kuma tabbatar da bin koyarwar addinin Musulunci.
KU KARANTA: Gwamnatin Kano Ta Bude Karbar Korafe-korafe Kan Aiyukan Hukumar KNUPDA
Ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna yadda wannan sana’a ke taimakawa wajen yaɗa fina-finai da bidiyoyi masu ɗauke da abubuwan da suka saɓa wa addini, al’ada da kyawawan ɗabi’u.
Mujahid ya ce saboda haka ne hukumar ta yanke shawarar dakatar da wannan sana’a domin kare matasa daga gurɓacewar tarbiyya da kuma rage yaɗuwar abubuwan da ke haddasa lalacewar zamantakewa.
Shugaban ya gargaɗi masu gudanar da sana’ar da su gaggauta dakatar da ita, yana mai cewa hukumar za ta ɗauki matakan doka kan duk wanda aka kama yana ci gaba da gudanar da aikin bayan wannan sanarwa.