• Wed. Oct 21st, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Pantami Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na PDP a Gombe

BySani Magaji Garko

Sep 29, 2026

Tsohon ministan sadarwa na kasa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaɓen dan takarar Gwamnan Jihar Gombe na Jam’iyyar PDP.

Pantami ya samu nasara a dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar, inda ya doke sauran ’yan takarar da suka fafata da shi a zaɓen.

Khamisu Ahmed Mailantarki ne ya zo na biyu yayin da Usman Aliyu Garry ya zo na uku.

KU KARANTA: Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Gwamnan Pantami a PDP

An gudanar da sabon zaɓen ne a yau Talata, 29 ga Satumba, 2026, bayan hukuncin babbar Kotun Tarayya da ke Gombe, wadda ta soke zaɓen fidda gwani na farko da ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar PDP na gwamnan jihar a zaɓen 2027.

Kotun ta umarci jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani cikin wa’adin da ta ƙayyade, bisa dokokin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokar zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *