Kwamitin kar-ta-kwana na yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi da daba a jihar Kano, karkashin jagorancin barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya samu nasarar kama wani hamshakin me ta’ammali da kayan maye dauke da kwalaben kodin guda 151 a dakinsa tare da gurfanar dashi a gaban kotu.
Kotun mai lamba 44 da ke Gwammaja a Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Muhammad Alhaji Isa, ta yanke wa Jabiru Umar Sanda Zage hukuncin ɗaurin shekara ɗaya kan samunsa da kayan maye, da kuma wata shekara ɗayan kan laifin ajiye mata a ɗakinsa.
Lauyan da ya gabatar da shi a gaban kotun, Auwal Abdulkadir Sani ya bayyana cewa kwamitin ƙar-ta-kwana dake yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi na Kano ya kama shi da kwalaben kodin 151 a ɗakinsa tare da mata uku cikin maye.
KU KARANTA: Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
An gurfanar da shi bisa zargin shiga ƙungiyar masu aikata laifuka, ta’ammali da kayan maye, bai wa mata da masu aikata laifuka mafaka, da kuma damun jama’a.
Kotun ta yanke hukuncin ne kan laifukan kayan maye da ajiye mata a ɗakinsa.
Sai dai bayanan da aka samu ba su fayyace ko zai yi zaman ɗaurin a lokaci guda ko ɗaya bayan ɗaya ba ne.