• Sun. Aug 23rd, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Shugaban K/H Kabo Ya Sauke Sakataren Mulki, Kansiloli 4 Saboda Tallata Tinubu

BySani Magaji Garko

Aug 11, 2026

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Hon. Lawan Najume Kabo ya sauke Sakataren Mulki na Karamar Hukumar da nadaddun Kansiloli huɗu, Saboda Shiga Ƙungiyar Tallata Shugaba Tinubu Da Sanata Barau (TMS) a Jihar Kano.

Lawan Najume Kabo ya bayyana hakan ne a zaman Majalisar karamar hukumar ta Kabo da aka yi a yau.

KU KARANTA: Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA

Wadanda aka sauke sun hada da Sakataren Mulki na Karamar Hukumar Kabo Abba Salisu Me wake Garo, da Kansilan me gafaka, Hon. Ahmad Yusuf Chiroma Godiya sai me ba shi shawara kan harkokin Ilimi Hon. Tanimu Garba Garo me ba shi shawara kan harkokin Ilimi da kuma Yakubu Sa’adu Gammo me ba shi shawara kan harkokin Addini.

An sauke su ne a wani taron gaggawa da Shugaban Karamar Hukumar Kab Hon. Lawan Najume ya Jagoranta da yammacin wannan Rana.

Haka kuma Kansilolin yankin sun tabbatar da sauke sun da shugaban yayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *