1- Duk da yake dai Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Abdulmumin Jibrin Kofa kwanannan zai bada cikakken bayani akan abin da ya faru, sannan kuma zai yi bayani kan ayyukan da yayi da empowerment da tallafi da kullun sai yaba mutane a kiru da Bebeji da kuma irin wakilcin da yayi wa al’ummar Kiru/Bebeji, haka zalika zai yi karin haske akan kyakkyawar mu’amalarsa da mutanen Kiru/Bebeji harda magabata da iyalansu. Duk Kofa zai biyo bayanansa da sheda a wuraren da suka dace musammanma ayyuka, gyaregyare da empowerment. Duk wanda yasan Kofa ba mai son fadin alherinsa bane saiya zama dole. Wannan bayanan da kofa zaiyi cikin kwananan in karyane, kofa yace kada Allah SWT Ya bashi nasara a zaben da zaayi kuma kada Allah SWT Ya biya masa bukatunsa duniya da lahira.
2- Duk mutanen da suke yada karya, cin mutunci da zarafin Kofa da kuma cewa baiyi aikin komai ba da mumunar wakilci su sani zasu tsaya a gaban Allah SWT.
3- Mutane su sani Allah (SWA) zai yi wa Kofa hukunci akan wakilcin da aka zabe shi 2011–2015, daga 2015–2016. Kowa ya san Kofa shekara daya kawai yayi a Majalisa a hawa na biyu, kuma kowa ya san abubuwan da suka faru don ya tsaya akan gaskiya. Sai da zaben 2019 ya gabato kotu ta maida Kofa Majalisa. Aka sake zaban Kofa hawa na uku 2019, wata shida kacal yayi a Majalisa sannan aka yi abin da aka yi aka raba shi da kujerarsa aka bawa Ali Datti. Saboda haka Ali Datti ne yayi wannan term din 2019- 2023. Amma harda zamani Hon Ali Datti an daurawa kofa akansa. Sai kaji mutum ba tsoron Allah yana cewa an zabe kofa yana kan kujera tun 2011 har 2023.
4- An sake zaban Kofa 2023 hawa na hudu. A yanzun yayi shekara biyu da watanni, bai ma cika shekara uku ba sai a watan gobe. Kuma cikin kwanakin nan kofa ya shirya saf zaiyi wa Jama’ar kiru/Bebeji cikakken bayani akan wakicin sa tsakanin sa da Allah SWT. Mutane su sani cewa za su mutu su hadu da Allah (SWA).
5- Kofa a zahiri an zabe shi sau hudu amma a zaman Majalisa ya yi kimanin shekaru takwas a cikin shekaru goma sha shida da ya kamata yayi. Kuma shekarun nanne Allah SWT zai masa hukunci akai. 2011–2015 shi ne kawai cikakken zamansa a Majalisa. Sauran lokuta an zabe shi amma bai yi cikakken zaman Majalisa ba. 2015-2019 bai kammala ba, haka kuma a zahiri 2019- 2023 bashi ya wakilce kiru da Bebeji ba, Hon Ali Datti ne. Dan Adam zai iya hukunci, amma abin farin ciki da jin dadi shi ne Allah ma zai yi nasa hukuncin.
6- Akan maganar fidda dan takara, ya zama wajibi a bada wannan bayani domin mutane su fara sanin gaskiyar abin daya faru kafin kofa yayi nashi cikkaken bayani. Amma kowa ya sani Kofa yace a shirye yake ayi sulhu ko primaries don yasan da ikon Allah zaiyi nasara. Kuma matsayarsa kenan harwa yau.
7- Mai girma Abdullahi Umar Ganduje, tare da Mataimakin Gwamna Hon. Murtala Sule Garo, Nasiru Aliko Koki, Kawu Sumaila da sauran jagororin tsohuwar (APC) sunyi nazari na tsahon lokaci akan Kofa da Majidadi, inda suka yanke hukuncin cewa a bar wa Kofa kujerar Majalisar Tarayya har zuwa lokacin da zai samu matsayi a gwamnatin tarayya.
8- Shi kuma Majidadi, kasancewar Mai Girma Gwamna ya bayar da guraben kwamishinoni, MD’s, Advisers da SA’s jagororin tare da Kofa su tabbatar da cewa Majidadi ya samu kujerar kwamishina.
9- A dalilin haka ne Kofa da Majidadi suka gudanar da zama har sau uku (3), tare da shaidar wani jagora a Kiru/Bebeji, inda suka cimma kyakkyawar fahimta a tsakanin su.
10- Daga nan ne Kofa ya shiga aiki ba dare ba rana wajen neman a baiwa Majidadi kujerar kwamishina. Kuma Majidadi da shi jagoran sunsan haka. Babu Masu hakkı a wannan kujera wanda Kofa bai kai masa kokon bara domin a baiwa Majidadi kujerar kwamishina Ba. Irin su Maigirma Gwamna, Ganduje, Murtala Garo, Kawu Samaila, Nasiru Aliko koki da sauran su.
11- Bayan haka, dan kar a samu matsala, Mai girma Ganduje da Mataimakin Gwamna, Murtala Garo da sauran jagororin tsohuwar APC suka kira wani zama na musamman wanda aka gayyaci wasu jagororin kano ta kudu wadanda suke da bukatar a baiwa candidate dinsu kujerar kwamishina. Sen Kawu Sumaila, Abdullahi Rogo, Alhasan Ado Doguwa, Mariya Bunkure, Nasiru Aliko Koki duk suna wajen.
12- A wannan meeting din ne akai ta bugawa da Kofa har ya kai ga saura kadan Kofa da Alhasan Ado Doguwa su bawa hamata iska, domin Kofa yayi tsayin daka akan Majidadi, Alhasan shima yana da nasa wanda yake so. A zamanne aka bada shawara cewa daya ya karbi kwamishana daya kuma a bashi MD. Amma kofa yace dole a baiwa Majidadi Kwamishana. Daga karshe akayi nasara domin aka ce toh su biyun za’a nema alfarma wajen Mai girma Gwamna ya kara slot daya saboda wannan rigimar da ake fuskanta, dan Majidadi ya samu kwamishana shima wancan na Alhassan Doguwa ya samu. Haka aka tashi taro, ma’ana anan shine su biyun za’ai wa kwamishina.
13- Tun ma kafin nan, Kofa ya kira Majidadi suka zauna, inda ya gaya masa cewa shima, Majidade yaje wuraren wadanda shi kofa yayi wa magana, domin shima Majidadin yayi masu godiya sannan kuma ya nemi alfarma. Akwai wani jagora a Kiru wanda ya raka Majidadi, suka ga wadannan mutane kuma sukayi masu magana.
14- Ita wannan yarjejeniya da akayi tsakanin shugabanni da jagororin tsohuwar (APC) dama shi Majidadi yasan haka cewa idan aka zo gaba na fitar da dan takara na consensus, a wannan gaba zai janye wa Kofa.
Haka akayi babu wata matsala a tsakanin su, aka kulla amana sannan aka cigaba da mutuntaka.
15- Da shugabanni a Kano suka bada umarni cewa caucus su kira taron consensus domin aje a ga yadda za’a fidda ‘yan takara, sai Kofa ya lura cewa Majidadi bai dauko hanyar zancen janyewa ba, kuma bayanai da suka biyo baya sun nuna cewa shi Majidadi ne ya rinka zuga wasu yan takara karsu janye. kuma kamar ma magoya bayansa basu san me akayi ba na amana tsanin Majidadi da Kofa ba. Amma duk da hakan, wannan abin bai dami Kofa ba, suka cigaba da magana da Majidadi a duk wadannan kwanakin suna waya, sannan idan sun hadu a wajen meeting na sulhu duk gaba daya suna tattauna wadannan abubuwa.Kuma dashi da Majidadi tsakanin su da Allah sun san abin da akayi.
16- Da aka gama meeting na farko, wasu suka janye wa Kofa, sauran su bakwai (7) suka ce baza su janye ba. Kofa baiyi fushi ba sai Kofa yace toh abi umarnin da aka bayar daga Kano ayi report wadanda basu janye ba sai a rubuta sai a kai wa kwamitin koli a Kano ta yanke hukunci wanda dama umarnin da aka bayar kenan daga Kano.
17- Saboda haka Majidadi ya bada shawara cewa hanzarin me ake yi tunda akwai gobe akwai jibi. Aka yi kokarin jawo hankalin sa cewa an bada umarni daga Kano cewa dole ranar Lahadi a kai report. Amma Majidadi ya tsaya akan shawararsa. Gida ta yarda. Sai akace wadannan su bakwai su kara haduwa washe garin.
18- Washegarin jagororin Kiru/Bebeji suka kara kiran taro. Wadannan ‘yan takara su bakwai (7) da Kofa suka sake haduwa, aka buga aka buga babu wanda ya janye kuma babu wanda ya janye wa wani.
19- Da aka gama bugawa Kofa ya sake bada shawara tunda babu alamar wani zai janye wa wani, abin da ya kamata ayi sai ayi report kamar yadda aka bada umarni ayi a Kano washegari a kai report.
20- A ranar kuma Majidadi yace hanzarin me ake yi, aka sake jan hankalin sa cewa goben nan Lahadi ance a kai report, ya nace cewa ba dole bane shugabanni daga Kano su nemi report a ranar Lahadi ba.
A haka aka tashi a ranar.
21- Washegari ranar Lahadi sai ga kira daga shugabanni daga Kano karfe goma na safe (10am) duk Local Government da constituency su kawo report. A wannan lokacin Kofa ya sake bugawa Majidadi waya yace kaga abin da na fada maka kar muyi masu laifi a Kano, tunda yake dai ba a daidaita ba. Duk wadanda suka rage a hada gaba daya a rubuta abin da ya faru kar a sa karya ko digo daya a mika masu a Kano suyi hukunci.
22- Shi kenan aka tafi ofishin Abdullahi Sa’idu karkashin shugancin Ciyaman na consensus, Hon Ali Mekaraye suka je suka rubuta report wanda ainahin gaskiyar abin da akayi ba cuta ba cutar wa. aka rubuta report abin da ya faru.Aka dauka aka kai Coronation, da aka kai Coronation Ali Mai Karaye ya fara kiran sunan ‘yan takara da ‘yan caucus duk su fara sa hannu.
23- Wannan ne yasa Kofa ya tashi, tunda yake dai babu wata rigima a taron babu wanda yake tunanin wani zai kawo wani abu da zai kawo tashin hankali. Kofa yaje Coronation yaje ya sanya hannu a wuraren da ake bukatar sa yasa hannu, bayan haka ya nemi kujera a gefe ya zauna.
24- Kwatsam ba ayi minti goma ba sai ga Majidadi ya shigo da magoya bayan sa da ‘yan daba da yan jagaliya, suka zo suna shiga suna bin gaban Kofa suna cin mutunci sa.
25- Dakin taron nan shugabanni da jagorori daga Kano gaba daya suna zaune a wannan dakin taro, hankali kwance babu wani tashin hankali. Sai gashi sun shigo, ba abin da suke yi sai cin mutuncin Kofa. Suka zagi Kofa, suka zagi iyayen sa, suka zage zuri’ar sa, suka ci mutuncinsa a idon al’ummar Jihar Kano.
26- sukaje wajen Ali Mai Karaye, yayi masu bayani, ya bawa Auwalu Dan Sharu report ya karanta masu abin da aka rubuta. Sai suka ce ba a saka Engr Salisu ba. Sai Ali Mai Karaye yace shi baya da wani receipt din Engr Salisu ya siya form, daga baya aka yanke hukunci aka ce a dauko biro a saka sunan Engr Kabiru Salisu dan a zauna lafiya.
27- Bayan an gama wannan, yaran Majidadi suka cigaba da cin mutuncin Kofa, suka zo har gaban sa suka wuce, akayi masa mummunan cin mutunci. Wani yaronsu ance sunansa, Maafuz ya fusge report a hannun Ali Mekaraye ya gudu dashi. Akwai shedar vidoe (Anyi kara wajen yan sanda kuma zaa hukunta shi ko ajuma ko a dade). Kowa a kano da Nigeria baki daya sunga bidiyo na irin cin mutuncin da akayi wa kofa dan a yada karya, aci zarafinsa kuma a nuna wa mutane a Kano da Nigeria cewa Jama’a basa tare dashi. Wannan cin mutuncin da akayi masa mummunan cin mutunci ne da duk mai hankali, duk mai daraja, duk wanda yake son kare mutuncin sa dole ya dau mataki na kare mutuncin sa.
28- Wannan dalilin ne yasa washegari Kofa, kasancewarsa cikakken dan siyasa, ya dauki matakai masu tsanani ba wai dan ya ci mutuncin kowa ba, sai dai dan ya kare mutuncin sa, domin tabbas wadannan mutane zasu iya dawowa suyi abin da suka yi a jiya.
29- Dan haka aka sake komawa wajen Mai Girma Gwamna bayan ganawa dashi karo na farko inda ya bada umarni caucus suje su dawo masa da suna daya ko biyu kawai. Caucus suka sa zama karfe biyu washe gari. Aka sanar a gaban Gwamna. Caucus Suka tabbatar da cewa an jira daga karfe biyu har karfe bakwai don kowa ya samu zuwa. Bayan jira, Sai caucus suka zauna da jagorori suka gudanar da zabe suka fidda ‘yan takara gaba daya a dunkule, kan su a hade suka fito da Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa a matsayin dan takarar Majalisar Wakilai, Hon. Kabiru Dashi a matsayin dan Majalisar Jiha mai wakiltar Kiru, da kuma Hon. Ali Muhammad Tiga a matsayin dan takarar Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Bebeji. Bayan gudanar da zabe sannan aka kai wa Mai Girma Gwamna.
30- Mai Girma Gwamna ya nuna farin cikin sa da irin hadin kai da mutanen Kiru/Bebeji suka yi, ya jinjina wa jagorori sannan ya mika form ga dan majalisar tarayya da ‘yan majalisar jiha. A lokacin da za mu fita, sai ga Majidadi ya shigo dakin taro ya samu Mai Girma Gwamna.
31- Bayan mun fita, Mai Girma Gwamna yace a fada mana mu dawo. Gwanma yace wa kofa abin da yake birge shi shine cewa Majidadi ya gaya masa yana da kyakkyawar alaka kuma akwai mutumtaka a tsakaninshi da Kofa sosai. Sai ya ce to meye matsalar a tsakanin ku?
Sai kofa ya fada wa Mai Girma Gwamna cewa tabbas Majidadi bai gaya masa abin da ya faru shekaran jiya ba. Kofa kuma ya gaya wa Gwamna cewa tabbas akwai wannan zaman lafiya a tsakaninsu, amma abin da ya faru shekaran jiya na cin mutunci da Majidadi yasa akayi masa haka kawai shi ne yasa aka samu matsala a tsakanin su.
32- Sai Mai Girma Gwamna yake fada musu duk a gaban Majidadin cewa Majidadi ya fada masa har akwai wata yarjejeniya da aka yi za’a samu masa kwamishana. To abin ya ba Kofa mamaki bayan abin da Majidadi yayi masa na cin mutunci da yakan takarar sa da kin zuwa wajen taron sulhu na uku a bisa umarnin Gwamna amma duk da hakan yana sha’awar a zo a tsaya a wannan yarjejeniya?
33- sai Kofa ya fadawa Mai Girma Gwamna cewa bashi da wata matsala, duk abin da za a yi wa Majidadi bashi da wata damuwa. Mai Girma Gwamna ya kara da cewa Kofa ya jawo kowa jikinsa. Gwamna ya kuma baiwa kowa hakuri kuma yace muyi hannu.
34- Kowa dai ya sani, duk wani dan Kiru/Bebeji ya san cewa Majidadi bai taba taimakawa Kofa ba a siyasa ko zabe tun 2011 zuwa yau. Adawa yake yi da Kofa, a duk wata fuska idan ka kalle shi ba adawa ba ce kawai, hassadace da kiyayya yake nuna wa Kofa. Kofa ya yi hakuri da wannan abu, amma Majidadi ya riga ya fito ya nuna wa Kofa cewa shi makiyin sa ne. Amma kuma Kofa a kullu yaumin yana barin Majidadi da Allah, har wa yau ya bar Majidadi da Allah.
35- Allah Ya kara wa Kofa karfin gwiwa da juriyar zuciya a duk abin da yake yi na alheri. Ina kira ga Kofa kar ya damu da yadda wasu mutane suke gani ko rashin fahimtar kokarin da yake yi, domin Allah Shi ne mafi sani kuma mafi adalci.
Allah Ya saka wa Kofa da alheri mai yawa, Ya bude masa kofofin nasara, Ya kuma kara daukaka darajarsa a dukkan lamura.
Allah ya raba shi da mahaifa lafiya Ya kuma kara musu lafiya, natsuwa da albarka a rayuwarsu, amin.
Abubakar Isa Ba’awa
Kungiyar Maliya youth.