• Sat. May 16th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Alhassan Ado Ya Yi Kiran Hadin Kai a Doguwa/Tudun Wada, Ya Bukaci a Sake Zaben APC Daga Sama Har Kasa

BySani Magaji Garko

May 13, 2026

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya yi kira ga daukacin mambobin Jam’iyar APC a yankunan Doguwa da Tudun Wada da su hada kai tare da mantawa da duk wani sabani domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabukan shekarar 2027.

Doguwa ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar ranar Laraba wacce shi da kansa ya sanyawa hanu, inda ya jaddada cewa lokaci ya yi da dukkan ‘ya’yan jam’iyyar su mike tsaye wajen kare muradun APC tare da tabbatar da nasarar ta daga sama har kasa.

Ya ce babu wani dan jam’iyya da yake dauka a matsayin bare a yanzu, yana mai cewa kowa nasa ne kuma a shirye yake ya yi aiki tare da kowane bangare domin ci gaban jam’iyyar.

KU KARANTA: Matsayar Abdulmumin Kofar Kan Fitar Da ‘Yan Takarar Majalisar Wakilan Kiru/Bebeji Da Kuma Turka-Turkar Siyasar Yankin 

Dan majalisar ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa irin karamci da goyon bayan da yake bai wa mambobin jam’iyyar, yana mai tabbatar da cewa ba za su ba gwamnatin kunya ba.

Hakazalika, Doguwa ya bukaci tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar da sabbin wadanda suka shigo APC tare da gwamnan jihar da su kara hakuri da juna tare da karfafa hadin kai domin cimma manufofin jam’iyyar.

Ya kuma yi kira ga duk wadanda suka fice daga APC saboda wasu dalilai da su dawo gida domin hada karfi da karfe wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki daya.

A bangaren siyasar kasa kuwa, Doguwa ya bukaci al’ummar Arewa da su fito kwansu da kwarkwatarsu wajen sake zaben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, a wa’adi na biyu domin ya kammala zangonsa na shekaru takwas.

Ya ce hakan zai tabbatar da adalci da daidaito tsakanin yankunan Arewa da Kudancin Najeriya, kamar yadda Arewa ta samu goyon baya a lokacin mulkin marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Doguwa ya bayyana cewa hadin kai tsakanin mambobin APC shi ne babban makamin da zai tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabuka masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *