Gwamnatin Jihar Kano ta ce burinta shine gina Al’umma mai cike da tsaro da tsari da tsafta da Aminci da kuma bunkasa tattalin arzikin mazauna ciki da wajen Jihar baki Daya.
Gwamnatin ta kuma Kaddamar da yaki ga mutane da suke sata gami da siyar da filayen gwamnatin, tana mai cewa a yanzu haka akwai Wandanda kotu da aike da su gidan yari kuma aka kwace filayen da suka siyar.
Kwamishinan Kasa da tsare-tsare na Jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar Garko ne ya bayyana hakan a jawabinsa lokacin mika takaddun filaye ga Kungiyoyin “Yan Akwatu”, taron da ya gudana a gidan gwamnatin Jihar Kano.
KU KARANTA: Gwamnatin Kano Ta Bude Karbar Korafe-korafe Kan Aiyukan Hukumar KNUPDA
Abduljabbar ya ce wannan kadara ce da zata cigaba da amfanar da wadanda suka bawa da ma iyalansu, a don haka yakamata su rike filayen hanu bibiyu domin cigaban Iyalansu baki Daya.
“Burin wannan gwamnati shine a rage yawan karancin gidaje da Kara yawan masu mallakar gidaje da samarwa da Iyalan mutanen Kano tsaro da kwanciyar hankali, tare da bawa mutanen Kano damar mallakar kadarorin da zasu amfane su da ‘ya’yan su a yanzu da nan gaba,” inji Abduljabbar.
“Wannan ya tabbatar da cewa gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, gwamnatin ce mai cika alkawari, ku sani wannan ba filaye kawai aka baku ba, sai dai filaye a cikin tsararrun guraren da suke da tsaro da inganci da ainihin takaddu wanda gwamnatin Jihar Kano ta amince da su, da kuma guraren da suke da Asibitoci da ofisoshin jami’an tsaro, da Masallatai, Makarantu da kuma guraren shakatawa” inji Kwamishinan.
Kwamishinan ya kuma bukaci wadanda suka amfana da kada su sayar da filin domin anyi hakan ne da nufin sama musu gidaje masu inganci da ma iyalansu.
A jawabinsa, gwamnan Jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf wanda Kwamishinan bibiyar ayyukan gwamnatin Jihar Kano Dakta Nura Iro Ma’aji ya wakilta ya bukaci wadanda suka amfana da su cigaba da jajircewa wajen yada ayyukan gwamnatin Kano.
Ya ce suna da rawar da zasu taka domin samun nasarar Jam’iyar APC a Jihar Kano da ma Nigeria, saboda haka basu filayen ya zama zasu sake saka Damba don tallata ayyuka da kare muhibba da darajar gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf da jami’an gwamnatin sa.
Taron ya sami halartar mai bawa gwamna shawara a harkokin siyasa Mustapha Hamza Buhari Bakwana da shugaban hukumar KINGIS Dakta Dalhatu Aliyu Sani da Kwamishinan shara’a da kuma sauran jami’an gwamnati.