• Sun. Aug 23rd, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA

BySani Magaji Garko

Aug 6, 2026

Gwamnatin Jihar Kano ta rushe wani dogon gini da ake ginawa a Unguwar Nassarawa GRA cikin kwaryar birnin Kano sakamakon saɓawa dokokin tsare-tsaren gine-gine da kin bin umarni.

Ma’aikatar Kasa da tsara Gine-Gine ta Jihar Kano ta rushe ginin a unguwar Nassarawa GRA, kusa da titin AVM Mukhtari Muhammad, bayan an tabbatar da cewa ya saɓa wa dukkanin ƙa’idodin tsare-tsaren gine-gine da aka amince da su a jihar.

A cewar Ma’aikatar, wanda ke gudanar da aikin ginin ya yi watsi da umarnin hukuma na dakatar da aikin duk da gargaɗin da aka yi masa sau da dama, lamarin da ya sa gwamnati ta ɗauki matakin tabbatar da bin doka.

KU KARANTA: “Burinmu Shine Gina Kano Mai Tsari, Tsaro, Tsafta, Aminci Da Cigaban Al’ummar  Ta” — Kwamishinan Kasa

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta ta kare babban tsarin bunƙasa birane na jihar (Master Plan), tare da gargaɗin cewa duk wani gini da ya saɓawa ƙa’ida zai fuskanci irin wannan mataki domin tabbatar da an bi doka da oda.

Idan za a tuna a satin nan Shugaban Kwamitin kar-ta-kwana mai binciko gine-gine da aka yi su ba bisa ka’ida ba, Dr Dalhatu Aliyu Sani, ya ce daga kafa kwamitin sun binciko gurare da akai gine-gine ba bisa ka’ida ba sama da 300 tare da umartar su dakatar da aikin har sai sun cika dukkan shawarwari da ka’idojin da gwamnati ta shimfida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *