Kantin Wellcare ya Nemi Afuwar Gwamnatin jihar Kano bayan rufeshi da Gwamnatin ta yi samakon matakin da ya dauka na dena karbar tsohon kudi.
A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar kula da kare hakkin Mai siye da Mai siyarwa ta jihar Kano ta aikowa GLOBAL TRACKER ta ce kantin ya dena karbar tsohon kudin ne daga ranar 10 ga Watan Fabarairun, 2023.
Sanarwar ta ce kwamitin karta Kwanar karkashin jagorancin Dakta Baffa Babba Dan-agundi ta ce kwamitin ya sami ingantaccen labari cewa kantin na Wellcare ya dena karbar tsofaffun kudi na Naira 200 da 500 da kuma 1,000.
Sanarwar ta bayyana cewa “Kantin Wellcare dake kan titin Murtala Muhammad ya rubutawa gwamnatin Jihar Kano takardar neman afuwa sakamakon rufe kantin da gwamnatin tayi bisa daina karbar tsofaffin kudade da gwamnatin tarayya ta canzawa fasali.”
“Kantin umarci ma’aikatansa ne da su daina karbar tsofaffin kudaden daga ranar goma ga watan Fabrairun da ta gabata”.
“Kantin ya bayyana cewa yayi kuskuren bayar da wannan umarni ga ma’aikatan nasa a don haka ya nemi afuwa daga gwamnatin da nufiin cewar hakan ba zata sake faruwa ba.”
Shugaban kwamitin Kar-ta-kwana na hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa Dr Baffa Babba Dan Agundi yace gwamnati ya samu ingantaccen labari akan cewar kantin na Welcare ba ya karbar tsofaffin naira 200 da 500 da naira kuma 1000, a sakamakon haka gwamnati ta bai wa kwamitin umarnin rufe kantin nan take.”
“Dr Baffa Babba Dan’ Agundi yace yin hakan saba doka ne domin har yanzu gwamnati ba ta dakatar da karbar tsofaffin kudaden ba.”
“Ya ja hankalin al’umma da su cigaba da hakuri dangane da halin da aja tsinci kai a ciki.”
Allah ya kyauta